Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin hutu don bai wa ma’aikatan Jihar da na Kananan Hukumomi damar tarbar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Al’adu da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Alhaji Sani Kabomo, ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina.
- Sabbin kudi: Makiyaya sun roki Buhari ya kori Gwamnan CBN
- HOTUNA: Yadda mutane suke dafifin cirar sabbin kudi a bankuna a Kano
Ana sa ran shugaba Buhari zai je Jihar ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta aiwatar.
Sanarwar ta bayyana cewa kwanakin aikin ba za su shafi ma’aikatan da ke cikin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, bankuna da masu samar da masu gudanar da wasu ayyukan na musamman ba.
Haka kuma ta bukaci ma’aikatan da abin ya shafa da sauran jama’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar Shugaba Buhari da mukarrabansa a Jihar.
Kabomo, ya kuma shawarci jama’ar Jihar da su nuna wa Buhari da ayarinsa karamci a matsayinsa na dan gida a yayin ziyarar.