Gwamnatin Jihar Kano ta umarci a rufe Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari da ke birnin Kano bayan kusan shekara uku da bude asibitin.
Sanarwar na zuwa ne bayan kotu ta ba kamfanin Northfield Health Services, da ke gudanar da asibitin, kwana takwas ya tattara nasa ya fice daga asibitin.
- Farouk Lawan ya kwana a Gidan Yarin Kuje
- An cafke dan aikin shugaban kungiyar ISWAP
- Za a kara wa ’yan sanda albashi
Sanarwar sallamar kamfanin na zuwa ne duk da kwantiragin shekara shida da suka rattaba hannu tsakaninsa da gwamnatin jihar bai kare ba.
Wani ma’aikacin asibitin ya fada wa Aminiya ranar Talata cewa umarnin kotun ya zo ne a ranar Litinin cewa hukumar gudanar da asibitin ya fice daga asibitin cikin kawana takwas.
Ya ce an dakatar da kusan kowane aikin kula da marasa lafiya an kuma rufe dakunan kwantar da marasa lafiyar, aka kuma hana kowa zuwa can.
“Bai kamata gwamnati ta jinginar da kowane aiki ba saboda ceto rayukan mutane,’’ inji majiyar.
Hukumar Kula da Asibitocin ta Jihar Kano ce za ta karbe ragamar gudanar da asibitin, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.
Wadansu ma’aikatan asibitin ma sun tabbatar da rufe asibitin inda suka ce suna kula ne da wadanda za su iya dubawa kawai a halin yanzu.
“Babu wani abu da mutum zai iya yi. Ai ka san umarnin kotu yadda yake, dole ne kawai mutum ya bi umarnin,” kamar yadda suka shaida wa Aminiya.
“Muna kokarin sallamar wadanda suke da dan dama dama. Wadanda suke jin jiki kuwa muna nan muna ta lallaba yadda za mu kula da su zuwa wani lokaci.”
Ko da wakilinmu ya ziyarci asibitin a ranar Talata, ya tarar da wadansu suna daukar bidiyon asibitin kuma ana gudanar da aiki har zuwa karewar wa’adin kwana takwas da kotun ta bayar.
Sai dai wani jami’in da bai bukaci a bayyana sunansa ba ya ce amshe ragamar gudanar da asibitin daga kamfanin zuwa Hukumar Kula da Asibitocin jihar ya saba wa kwantiragin shekara shida da gwamnatin ta rattaba hannu da kamfanin na Northfield Health Services.
Northfield Health Services yana kokarin kalubalntar da hukuncin, sai dai ba a san yadda hakan za ta faru cikin wa’adin kwana takwas da aka dibar masa na ya fice ba.
“Lauyoyinmu na aiki a kai, batun na gaban kotu a halin yanzu; Ba za mu yi wani tsokaci ba tukuna har sai mun ga yadda za ta kaya a kotun tukuna,’’ a cewar wani jami’in kamfanin.
Wadansu da ke da masaniya kan batun sun ki cewa uffan a lokacin da Aminiya ta tuntube su, suna masu alakanta batun da bambance-bambancen siyasar cikin jam’iyyar da ke mulkin jihar.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa umarnin kotun wani shiri ne na siyasa kawai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake yi domin kara fadada ikon tafiyar da asibitin.
“Ka san wa’adinsa zai kare cikin shekara biyun da ke tafe wanda yake nufin kwantiragin ba zai kare ba har bayan wa’adin nasa; don haka ba zai iya yin wani katabus a kan asibitin ba idan har bai zo da wannan shirin nasa ba,’’ a cewar majiyar.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Tsanyawa, game da rufe asibitin, amma bai amsa kiran wayar da aka yi ta masa ba, tun maraicen Talata zuwa safiyar Laraba.