✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta haramta amfani da kwalekwalen haya a Bagwai

Gwamnatin ta ce za ta samar da motocin bas gida biyu domin jigilar mutane tsakanin garuruwan.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta amfani da kwalekwale na haya domin sufuri a ruwan Bagwai zuwa Badau da ke Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar.

Umarnin na zuwa ne kwana daya bayan wani kwalekwale da ke dauke da fasinjoji kimanin 47, yawancinsu dalibai, ya yi kife a ruwan, tare da kashe mutum 29 daga cikinsu.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya fitar da yammacin Laraba.

Sanarwar ta ce sakamakon daukar matakin, gwamnatin Jihar ta samar da motocin bas gida biyu domin jigilar mutane tsakanin garuruwan Bagwai da Badau.

Kazalika, gwamnatin ta kuma ce za ta sayi sabbin kwalekwale guda biyu domin saukaka musu zirga-zirgar.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnati za ta tabbatar da kafa tsauraran matakai, baya ga kaddamar da kwamitin bincike, wanda daga bisani zai mika shawarwarinsa ga gwamnatin.