Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da fitar da Naira biliyan 6.563 kuɗin giratuti domin biyan haƙƙoƙin ’yan fansho da suka yi ritaya daga shekarar 2021 zuwa 2023.
Wannan sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa karo na 48 wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.
- Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard
- Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump
Kwamishinan Kuɗi da Tattalin Arziki, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa Naira biliyan 1.954 za a biya a watan Oktoba ga waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2021, sai Naira biliyan 2.267 a watan Nuwamba ga waɗanda suka yi ritaya a 2022.
Sannan kuma za a biya Naira biliyan 2.342 a watan Disamba ga waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2023, kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
Da wannan mataki dai gwamnatin za ta cike gibin bashin kuɗin giratuti da Gwamnatin Inuwa Yahaya ta gada, wanda ya kai sama da Naira biliyan 21 a shekarar 2019.
“Zuwa yanzu, an riga an biya sama da Naira biliyan 17, wanda ke nuna jajircewar gwamnatin wajen kula da jin daɗin ma’aikata.”
Da wannan biyan na baya-bayan nan, gwamnatin na gab da kammala biyan dukkan hakkokin giratuti daga shekarar 2014 zuwa 2023, wanda ke tabbatar da alkawarin ta ga wadanda suka yi ritaya tare da dawo da amana tsakanin gwamnati da al’umma.