✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan siyasa sun mai da barayin gwamnati ’yan gata —IBB

IBB ya ce Yan siyasa sun bar jami'an gwamnatinsu da suka saci biliyoyi na yawo.

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ce kazantar rashawa a karkashin gwamnatocin ’yan siyasa a Najeriya ta ninka ta lokacin mulkinsa.

IBB ya ce gwamnatinsa ta mulkin soji ta yaki da rashawa fiye da gwamnatin ’yan siyasa na yanzu, wadanda ya ce sun sa barayin gwamnati sun samu sakewa.

A cewarsa, mutanen da suka yi aiki a gwamnatinsa ‘bayin Allah’ ne idan aka kwatanta su da jami’an gwamnatin ’yan siyasa.

A hirar da gidan talabijin na ARISE TV ya yi da Babangida a safiyar Juma’a, tsohon shugaban kasar ya ce gwamatinsa ta dauki mataki a kan wani gwamnan mulkin soji da ya wawure Naira 313,000, amma  yanzu ’yan siyasa sun kyale barayin biliyoyin Naira suna yawo, babu abin da aka yi musu.

Ya bayyana haka ne a lokacin da aka tambaye shi kan kallon da ake wa gwamnatinsa cewa ta yi kaurin suna wurin ayyukan rashawa.

A cewarsa, “Amma ai abin da ke faruwa yanzu ya fi kazanta a kan lokacin da muke kan mulki… ai mu bayin Allah ne ida aka kwatanta mu da su.”

– Najeriya na bukatar shugaba masanin tattalin arziki

Game halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu, Babangida ya shawarci Gwamatin Buhari ta sassauta tsare-tsarenta a bangaren.

Ya ce, “An tsaurara tsarin gudanar da tattalin arzikin da ake amfani da shi a yanzu; Ya kamata a buda shi ta yadda za mu ci moriyar albarkatun da Allah Ya huwace mana.”

Ya ci gaba da cewa, “’Yan Najeriya na da basira da hazaka, ya kamata shugabanni su san yadda za su yi amfani da wadannan abubuwa domin cire kitse daga wuta.”

A kan haka ne ya ce duk wanda zai zama Shugaban Kasar a nan gaba, ya kamata ya kasance mai cikakken sani a kan sha’anin tattalin arziki.

Ya ce, “Ya kamata kuma shugaban ya samu zurfin fahimtar tattalin arziki kuma kasance kwararren dan siyasa da zai iya yi wa ’yan kasa bayani su fahimce shi da dai sauransu.”

IBB wanda ya ce ya san wasu masu wannan nagartar ya kara da cewa, “Idan aka samu shugaba wanda yake tare da mutane yake kuma sauraron su, ba mai magana da manyan mutane ba kawai, abubuwa za su gyaru”.

“Na fara hararo wasu shugabannin Najeriya na gaba masu nagarta. A samu mutumin da ya yi yawo a ko’ina a kasar, yake kuma da abokai a kusan kowane yanki, sannan yana ko da mutum daya ne da zai yi magana da shi a ko’ina,” kamar yadda ya kara.

“Ya kamata shugabanni su yi wa Najeriya da ma ’yan kasar kyakkyawan sani; Duk mai son zama shugaban mutane wajibi ne ya yi amfani da basirarsa wajen fahimtar su.”