Gwamnatin Borno ta ayyana ranar Litinin a matsayin hutu don bikin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446.
Muƙaddashin gwamnan jihar, Alhaji Umar Kadafur, ya sanar da cewa za a yi hutu a ranar Litinin a faɗin jihar.
Kadafur, ya ce sun bayar da hutun ne don girmama sabuwar shekarar Musulunci, wadda ta ke farawa a watan Muharram.
A cewarsa, hutun na nufin bai wa al’ummar Musulmi damar sanin muhimmancin kalandar hijira da kuma murnar sabuwar shekarar Musulunci domin samun haɗin kai da ƙauna a tsakaninsu.
Ya ce hijira ta nuna lokacin da Annabi Muhammad (SAW), ya yi ƙaura daga Makka zuwa Madina a shekarar 622 A.Z.
Muharram kuma na ɗaya daga cikin watanni huɗu masu daraja a kalandar Musulunci, kamar yadda Allah (SWT), Ya bayyana a cikin Alƙur’ani mai girma.
Muƙaddashin gwamnan, ya yi wa Musulmin Borno da ma duniya baki ɗaya fatan alheri, inda ya buƙaci a zauna lafiya da nuna ƙauna a zamantakewar yau da kullum.
Ya buƙaci al’ummar Musulmi da su kiyaye ɗabi’u na mutuntawa, kishin ƙasa da kuma karrama juna.
Kadafur ya buƙaci Musulmi da mabiyan sauran addinai, da su ƙarfafa alaƙar ‘yan uwantaka, karamci, jin-ƙai da sauran halaye nagari.