Gwamnatin Taliban ta Afghanistan da ta Amurka sun kammala musayar fursunoni a tsakaninsu, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Afghanistan, Amir Khan Muttaqi ya tabbatar.
Taliban dai ta mika wa Amurka wani gogaggen sojan ruwanta, Mark Frerichs, wanda aka sace a 2020, yayin da ita kuma ta mika Bashir Noorzai, wani makusancin shugabannin Taliban da aka daure shekara 17 a Guantanamo bayan an same shi da laifin safarar Hodar Iblis.
- Za a kara mafi karancin albashi daga N30,000 —Ngige
- NAJERIYA A YAU: Irin Asarar Da Cin Ganda Ke Janyo Wa Tattalin Arzikin Najeriya
A cewar Ministan ranar Litinin, “Yau ce ranar da aka mika wa Amurka sojan ruwanta, mu kuma suka mika mana Bashar a filin jirgin saman Kabul bayan doguwar tattaunawa,” kamar yadda ya shaida wa ’yan jarida a Kabul.
Sashen Harkokin Waje na Amurka ya ce an sace sojan ruwan nasu ne lokacin da yake aiki a matsayin injiniyan gine-gine a wajen wani aiki a Afghanistan.
An yi masa gani na karshe ne a wani bidiyo da aka fitar a farkon wannan shekarar, inda aka gan shi yana rokon a samu a akubutar da shi don ya samu ya hadu da iyalansa.
A cikin bidiyon dai, Mark ya ce an nade shi ne a watan Nuwamban bara.
Kakakin gwamnatin Afghanistan, Zabuhillah Mujahid, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) cewa Bashar ba shi da wani mukami a gwamnatin Taliban, amma ya taka muhimmiyar rawa a cikinta, ciki har da samar mata da makamai lokacin da aka kirkire ta a farkon shekarun 1990.
A wani takaitaccen taron manema labarai da ya gudanar tare da Muttaqi da kuma mai rikon mukamin Mataimakin Firaministan Afghanistan, Bashar ya ce yana farin cikin kasancewa a babban birnin kasarsa bayan tsawon lokaci.
Tun da Taliban ta sake kwace mulkin Afghanistan a 2021 dai Amurka ta juya mata baya tare da rufe wasu kadarorin babban bankin kasar da suka kai na Dala biliyan tara, in ban da a kwanan nan da ta ce za ta sakar musu Dala biliyan 3.5 saboda mutanen kasar.