Gwamnatin Jihar Adamawa ta sake yin gargadi ga jama’arta game da fita bayan sanya dokar hana fita a jihar, a yayin da mutanen jihar basu fasa yin barna wajen rusa rumbunan abincin ‘yan kasuwa ba.
Sakataren Labarai na fadar Gwamnatin Jihar, Humwashi Wonosikou ne ya tabbatar da wannan gargadin da gwamnan yayi a ranar Litinin yayin zanta wa da manema labarai.
- NAHCON ta fito da ka’idojin tafiya Umrah daga Nijeriya
- Gwamnatin Filato za ta hukunta mutanen da suka fasa rumbunan ajiye abinci
Ya ce, Gwamna Ahmadu Fintiri ya nuna rashin jin dadinsa game da dabi’un jama’a ta yadda duk da an sanya dokar hana fita, basu fasa rusa rumbunan abincin mutanen gari da na gwamnati ba.
“Gwamna Fintiri ya nuna rashin jin dadinsa game da irin barnar da ake yi a jihar kuma ya bukaci jama’a da su nutsu domin samun zaman lafiya.
Ya bukaci Jami’an tsaro da su gaggauta kawo zaman lafiya a jihar tare da yin gargadin cewa duk wanda ya karya doka, gwamnatin ba za ta rangwanta masa ba.
Gwamnan ya ce ba za a amince da zirga-zirgar ababen hawa ba har zuwa lokacin da za a janye dokar hana fita kuma duk wanda aka kama a kan hanya ya kuka da kansa.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Adamawa ba za ta bari bata bari su rusa zaman lafiyar da aka gina na tsawon shekaru da dama, inda ya ke kiran al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro domin cin nasarar a kan lamarin.
Ya bayyana wannan dabi’a ta fasa rumbunan a matsayin abin takaici, inda ya ke kira ga jama’a da su canza halayansu domin duk wanda aka kama zai yi kuka da kansa kuma babu ranar dage hana dokar fita.