Gwamnatin Abia ta jajanta wa al’ummar Jihar Gombe kan kisan fataken shanu da aka yi a babbar kasuwar shanu ta garin Aba da ke Abia.
Aminiya ta ruwaito cewa, makonni uku da suka gabata ne aka kashe fataken shanu 9 a babbar kasuwar kuma cikin su 7 ’yan asalin Jihar Gombe ne.
Bayanai sun ce tawagar da Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu ya tura ta isa Jihar Gomben ne a ranar Litinin, karkashin jagorancin Sarkin Inyamurai Enachioken of Abiriba, Mista Kalu Ogbu Kalu.
Da yake gabatar da sakonsa na jaje, Mista Kalu ya ce gwamnati da al’ummar Jihar Abia sun yi Allah wadai da lamarin kuma tuni Gwamnan Ikpeazu ya sha alwashin ganin an zakulo wadanda suka aikata kisan domin su girbi abin da suka shuka.
Ya kuma ce har yanzu akwai danganta ka mai kyau a tsakanin al’ummar jihar Abia da Gombe sannan ya yi kira ga al’ummar Gombe da su zo Gombe dan zuba jari, inda yake tabbatar da cewa za’a kare su.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Manasseh Daniel Jatau, ya yaba wa gwamnan jihar Abia bisa wannan karamci na aiko tawaga ta musamman don yi musu ta’aziya.
A cewarsa, Gwamna Ikpeazu ya yi abin da ya kamata na rage wa iyalan fataken shanun radadin rashin da suka yi.
“Akwai zaman lafiya a Jihar Gombe kuma yana da kyau ’yan kabilar Ibo mazauna Kudu su zo su zuba hannun jari saboda amince da muke da shi a jihar.”
A nasa bangaren, Mai martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya jinjina wa gwamnatin Jihar Abia kan yadda ta turo tawaga suka jajanta wa Gombawa da kuma rage musu radadi na irin asarar da suka yi, yana mai cewa matakin da gwamnatin ta dauka abun a yaba mata ne.
Alhaji Yahuza Yusuf, Shugaban Kungiyar Fataken Shanu a Gombe, ya yaba wa gwamnan Abia bisa wannan ziyarar jaje da ya turo tawaga ta musamman ta kawo jihar.
Yahuza, ya ce cikin mutane 9 da aka kashe 7 ’yan Gombe ne wanda gwamnatin Abia ta yi alkawarin bai wa iyalansu naira miliyan biyu amma dai har yanzu kudin basu iso ba.