Gwamnatin Jihar Yobe ta kudiri aniyar tallafa wa almajirai 12,000 daga makarantun tsangaya 240 a wadansu Kananan Hukumomi bakwai na Jihar.
Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA) na jihar Yobe, Dokta Muhammad Goje ne ya bayyana hakan a Damaturu, babban birnin Jihar.
- An bayyana Gwarazan Gasar Rubutattun Wakokin Hausa
- Yadda Hadurra ke lakume Rayukan Dubban ‘yan Najeriya
Hakan na zuwa ne yayin da Gwamna Mai Mala Buni na jihar ke kokarin tallafa wa masu karamin karfi da kungiyoyin gajiyayyu a lokacin bukukuwan Sallah, da ake shirin shaidawa a mako mai zuwa.
Goje, ya ce a ganin sa wannan kuduri ne na gyara tsarin almajiranci a jihar wanda ya kamata a yi koyi da shi don ciyar da almajirai gaba.
Wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati, tuni suka fara koyi da wannan tsari kamar yadda gwamnati ta umurci SEMA ta samar wa almajirai kayan sallah da sauran abubuwan walwala.
A cewarsa, duk wani almajiri da aka zaba cikin wadannan Kananan Hukumomi a ranar Sallah zai ci ya sha cikin nishadi ba tare da yaje bara ko ina ba.
Kazalika, ya ce za a ba almajiran da rabonsu ya tsaga sabbin kayan sallah da sauran abubuwan da suka kamata.
Aminiya ta lura cewa wannan shirin shi ne na farko da za a fara kuma ana harin Kananan Hukumomi bakwai ne da makarantun tsangaya 240 domin almajirai 12,000 su ci moriya.