✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati za ta lalata bindigogi 3,000 da ta kwato a hannun ’yan ta’adda

An kwace makaman ne a cikin wata 18 da suka gabata sassan Najeriya

Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA) ta hannun Cibiyar Kula da Makamai ta Kasa (NCCSALW), zai lalata bindigogi sama da 3,000 da aka kwace daga hannun ’yan ta’adda a sassan Najeriya.

Cibiyar ta ce an kwace galibin makaman ne a cikin wata 18 da suka gabata a shiyyoyin Arewa maso Yamma da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.

Da yake yi wa manema labarai karin haske kan batun a Kaduna, Shugaban Cibiyar NCCSALW na Kasa, Manjo-Janar Abba Muhammed Dikko (mai murabus) ya bayyana cewa, an kwace makaman ne a cikin watanni 18 da suka shude.

Ya ce hukumomin tsaro daban-daban kuma daga sassa daban-daban ne suka mika wa cibiyar makaman bayan da suka kama.

Ya kara da cewa, matakin lalata makaman na daga umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na inganta tsaro a fadin kasa.

A cewarsa, bindigogi kirar AK-47 da AK-49 da sauransu na daga cikin makaman da za a lalata din.

%d bloggers like this: