Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA) ta hannun Cibiyar Kula da Makamai ta Kasa (NCCSALW), zai lalata bindigogi sama da 3,000 da aka kwace daga hannun ’yan ta’adda a sassan Najeriya.
Cibiyar ta ce an kwace galibin makaman ne a cikin wata 18 da suka gabata a shiyyoyin Arewa maso Yamma da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.
- Kebbi ta Tsakiya: Zaben Sanata da zai fi na gwamna Zafi
- Dillalan kwaya 993 sun shiga hannu a Katsina
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan batun a Kaduna, Shugaban Cibiyar NCCSALW na Kasa, Manjo-Janar Abba Muhammed Dikko (mai murabus) ya bayyana cewa, an kwace makaman ne a cikin watanni 18 da suka shude.
Ya ce hukumomin tsaro daban-daban kuma daga sassa daban-daban ne suka mika wa cibiyar makaman bayan da suka kama.
Ya kara da cewa, matakin lalata makaman na daga umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na inganta tsaro a fadin kasa.
A cewarsa, bindigogi kirar AK-47 da AK-49 da sauransu na daga cikin makaman da za a lalata din.