Gwamnatin Jihar Bauchi ta kudiri aniyar aurar da masu sana’ar karuwanci a fadin Jihar yayin da duk wacce a cikinsu ta samu wanda ya fito neman aurenta da gaske.
Hakan na nuwa zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ta sanar da shirinta na gudanar da kidayar gano hakinanin adadin karuwai a Jihar domin samun duk wasu tabbattun bayanai a kansu.
Malam Aminu Balarabe Isah, Kwamishinan dindindin a Ma’aikatar Hisbah da Shari’a ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan karuwai da aka gudanar ranar Litinin a Bauchi.
A cewarsa, tattara bayanan zai taimaka wa hukumar wajen daukar matakan da za ta sanya karuwan su yi kasa a gwiwa da zummar hana su ci gaba da wannan mummunar sana’a mai cike da hadari.
Kwamishinan ya ce, daga cikin ababen da gwamnatin Jihar za ta aiwatar domin cimma wannan manufa, akwai shirin bayar da tallafi da kuma sama musu jari na shiga kasuwanci domin samun abin dogaro da kai.
Ya bayyana cewa, binciken da suka gudanar ya nuna cewa mafi akasari matan sun shiga karuwancin ne sakamakon rashin ilimi, talauci ko kuma azabtarwa da suka rika fuskanta a wajen iyayensu mata musamman kishiyar uwa.
Ya ce, kananan rikice-rikice a cikin dangi suna kuma taka rawar gani wajen jefa wasu matan cikin wannan mummunar sana’a, lamarin da ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen mayar da su wurin iyayensu.
Hafsat Azare, wadda ta yi magana a madadin sauran karuwan, ta bayar da tabbaci kan shirinsu na watsi da wannan sana’a madamar gwamnati za ta tallafa musu, inda ta bayyana halin da suka tsinci kansu a yanzu a matsayin abin a tausaya.