Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da bukatar neman sahalewar Majalisar Dokokin Tarayya don karbo bashin dala biliyan 1.2 daga kasar Brazil domin daukar nauyin shirye-shirye ayyukan noma da aka tsara a cikin kasafin kudin badi.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kudi na Majalisar Wakilai a ranar Talata domin kare kasafin kudin da ma’aikatarta ta gabatar da hujja a kan kudin da ma’aikatar za ta bukata a badi.
- Ba wanda zai yi rabin abin da Messi da Ronaldo suka yi a kwallo – Maradona
- Zaben Amurka: Neman tsayar da kirga kuri’u shirme ne —Biden
Ministar ta ce Gwamnatin Tarayya ta aike wa da Majalisar Tarayyar bukatar karbo bashin daga kasar Brazil domin inganta ayyukan noma a Najeriya.
Ta ce Gwamnatin Tarayya za ta mallaki hekta 100,000 ta gona duk jiha a Najeriya domin noma kayan abinci tare da gina hanyoyi a wannan wurare don samar wa manoma damar kai amfanin gona zuwa kasuwanni da rage asarar ta ke biyo bayan girbi.
A wata zanta wa da Ministan Noma na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono ya yi da BBC, ya ce za a karbo bashin ne domin zamanantar da aikin noma tare da inganta shi a kananan hukumomi 632 na kasar.
Minista Nanono ya ce za a yi amfani da wannan kudi wajen sayo motocin noma da kayan gyaransu da gina wuraren ajiye kayan feshi da magungunan kwari da sauransu.