Gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta wa ’yan kasarta tafiya domin shiga sahun mayakan Ukraine da zummar yakar dakarun sojin Rasha.
Wannan dai na zuwa a yayin da wasu rahotanni ke cewa an fara yi wa ’yan kasar ’yan sa-kai rijista domin su taimaka wa sojojin Ukraine a mamayar da Rasha ke yi wa kasar.
Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Francisca K. Omayuli ta fitar a ranar Litinin, ta ce ofishin jakadancin Ukraine da ke kasar ya musanta taka wata rawa a wannan abin takaicin.
Sai dai Ofishin Jakadancin na Ukraine ya bayar da tabbacin cewa wasu ’yan Najeriya sun sanar da shi cewa a shirye suke a yi wannan yakin da su.
Ofishin jakadancin ya kuma nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya bukaci dukkan dan Najeriyar da ke son shiga yakin da ya biya dalar Amurka 1,000 a matsayin kudin tikitin jirgin sama da na biza.
BBC ya ruwaito cewa, wannan matakin na Najeriya na zuwa ne bayan kwana daya da kasar Senega ta gargadi ’yan kasarta masu sha’awar tafiya Ukraine da su guji daukan wannan matakin.
Ta umarci jakadan kasar Ukraine da ya sauke wasu bayanai da ofishinsa ya wallafa a Facebook yana kira ga ’yan Senegal su yi rajista domin a tafi da su can su yi yaki.