✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta dauki ’yan sanda 50,000 aiki duk shekara — Shekarau

Tsohon gwamnan ya ce dole sai an yi tafiya da sarakunan gargajiya matukar ana so tsarin ya yi tasiri.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta dinga daukar ’yan sanda 50,000 aiki duk shekara matukar ana son kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Shekararu, ya bayyana haka ne a gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya yi tsokaci game da batun kirkirar ’yan sandan jihohi da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

“Shi (tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari), ya yi alkawarin daukar ’yan sanda 10,000 aiki duk shekara, amma rahoton kwamitina kan fansho ya nuna duk shekara ’yan sanda 5,000 na barin aiki ko don ritaya ko kuma wani dalili na daban.

“Idan kana daukar mutum 10,000 aiki ka ga ke nan, 5,000 kake dauka tun da wasu na barin aikin, ya kamata a fito da tsarin daukar ’yan sanda 50,000 ko 60,000 aiki ba tare da tsayawa ba,” in ji Shekarau.

Tsohon Sanatan, ya ce babu ta yadda ’yan sanda 300,000 za su wadata wajen samar wa da Najeriya tsaro.

Kazalika, tsohon gwamnan ya ce matukar gwamnati na son tsarin daukar ’yan sandan jihohi aiki ya yi tasiri, dole ne sai an sanya masu sarautun gargajiya a tsari.

“Abin da muke fada shi ne wadannan masu aikata laifin ba a duniyar wata suke ba, suna tare da mu, don haka dole a fito da tsarin sanya ido da samun bayanan sirri.

“Kada ka manta ba za mu iya yin hakan ba, ba tare da gudunmawar sarakunan gargajiya ba, shi ya sa Kano ta yi nasara ta wannan bangaren.”

Gwamnan ya yi bayani kan yadda aka kirkiro Hisbah a jihar, amma ya jadadda bukatar samar da jami’an tsaro daga al’umma wadda gwamnati za ta ke jagoranta.

Ya ce hakimai, da masu unguwanni na daga cikin tsarin kafa Hisbah wanda hakan ya sa hukumar yin tasiri a jihar.