Gwamnatin Tarayya, ta ƙaddamar da rabon tan 42,000 na hatsi ga mabuƙata a Jihar Sakkwato.
Rabon wani ɓangare ne na umarnin shugaba Bola Tinubu, na tallafa wa marasa ƙarfi da abinci a halin matsin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan ranar Lahadi a shafinsa na X (Twitter).
Ya ce “Na bi sahun gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu da abokan aikina, ministan noma da samar da abinci da ƙaramin minista Sabi Aliyu wajen ƙaddamar da rabon.”
Hukumar Bayar da Agaji ta Kasa (NEMA), za ta sanya ido kan rabon tare da taimakon hukumomin tsaro domin tabbatar da gaskiya da adalci.
A cewar ministan, kowace jiha a faɗin Najeriya za ta ci gajiyar rabon “Za mu tabbatar mun bayar da ƙarin bayani kan shirin.”
Tun farkon watan Maris ne, Shugaba Bola Tinubu, ya bayar da umarnin fara raba hatsin a faɗin jihohin Najeriya 36 da ke ƙasar nan.
Wannan dai na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi wata 10, bayan karɓar mulki a watan Mayun 2023.
Cire tallafin ya janyo hauhawar farashin kayayyakin masarufi, lamarin da ya kai ga gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin ƙasar nan.