✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ki saurari Sarkin Musulmi da sauran shugabanni

“Mun san cewa canji yana da matukar wahala, musamman canja abubuwan da suka dade a watse kuma a tabarbare. Mun ta gaya ma mutane su…

“Mun san cewa canji yana da matukar wahala, musamman canja abubuwan da suka dade a watse kuma a tabarbare. Mun ta gaya ma mutane su yi hakuri da wannan gwamnati, amma akwai iyaka akan ban hakurin, a lokacin da mutane suke fama da yunwa.” Wasu daga cikin kalaman mai alfarma Sarkin Musulmi ke nan Alhaji Muhammadu Sa`ad Abubakar, a lokacin da yake karbar bakuncin Kontarola Janar na Hukumar Kwastan Kanar Hamid Ali mai (ritaya), a fadarsa da ke Sakkwato birnin Shehu a cikin makon da ya gabata.
Mai alfarma Sarkin Musulmin yana nuna damuwarsa ne a kan irin yadda gwamnatin tarayya ta rurrufe kan iyakokin kasar nan na kasa, da a da ake shigo da abinci irin su shinkafa, amma kuma gwamnatin tarayyar ta rufe su da rana kwatsam. Mai alfarmar ya ci gaba da fada wa babban bakon nasa cewa “ Ku bude kan iyakokin kasar nan na kasa, domin saukaka wahalar da talakawan Najeriya suke ciki, yin haka da kyakkyawar manufa da neman samun sauki ga talakawa hakan ne bukatata, za mu dade ba mu samu biyan bukatar da muke so ba, matukar abinci yana wahala. . . Ku bude su tare da sanya idanu a rinka shigowa da kayan amfani ga jama`a, hakan zai kawo saukin wahalar da ake ciki” Mai alfarma Sarkin Musulmi ke nan a kan nemansa na a bari a rika da shigo da shinkafa ta kan iyakokin kasar nan na kasa.
Kamar sun hada baki, shi ma Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, lokacin da yake karbar bakuncin Kanar Hamid Ali (mai ritaya), irin wannan kira ya yi ga Hukumar ta Kwastam, da ta duba yiwuwar canja wasu daga cikin ka`idojin da ta dauka zuwa yanzu, ta yadda za su taimaka wa talaka wajen rage radadin mawuyacin halin da yake ciki. Gwamnan na Sakkwato ya ci gaba da fada wa babban bakon nasa cewa “Ina da yakinin ka san mawuyacin halin da kasar nan take ciki, don haka ina kira gareka koyaushe a rinka sa ka`idojin da za su yi sassauci ga jama`a. ” Gwamnan na Sakkwato ya kara da cewa rufe kan iyakokin na kasa wajen shigo da shinkafa, ya sanya ta yi muguwar tsada, ta yadda ba kowa ke iya sayenta ba, don haka sai ya roki Hukumar ta Kwastam ta sassauta hana shigowa da ita a iyakokin kasa, har zuwa lokacin da kasar nan take iya noma shinkafar da take bukata.
Tun tuni ba tun yau ba, shugabannin al`umma daban-daban suke ta irin wadancan kiraye-kiraye, musamman daga Jihohin Arewa, a kan lallai sai gwamnatin ta canja wancan tsari na hana shigo da shinkafar ta kan iyakokin kasar nan na kasa. Kiraye-kirayen da ba su rasa nasaba da irin tashin gwauron zabi da farashin shinkafar ya yi da kuma irin yadda ta zama cimakar kowa da kowa saboda saukin sarrafawa a kan sauran kayan abinci. Buhun shinkafa dai yanzu ya kai N14,000 zuwa N15, 000, sabanin bara a daidai wannan lokaci da bai wuce N7,500 zuwa N9,000.  
Ba wai hana shigo da shinkafa kwata-kwata ba gwamnatin tarayya ta yi ba, a`a ta kan iyakokin kasa ta haramta, bayan ta dan jarraba dode su a yan watannin baya, jama`ar yankin wannan bangaren sun dandana irin saukin da ake samu wajen shigo da shinkafar ta wadannan hanyoyi, sabanin ta tashoshin jiragen ruwa da suke Kudancin kasar nan. Bayanin da gwamnati ko in ce Hukumar Kwastam ta bayar a kwanakin baya da za ta hana shigo da shinkafar ta kan iyakokin kasar nan na kasa, shi ne wai masu shigo da ita din fasakwaurin ta suke yi, ma`ana, maimakon su biya kudin fito a kan ainahin na wayan shinkafar da suka shigo da ita, wai sai su hada baki da wasu jami`anta su rinka yin ojoro, wajen rage yawan wadda suka shigo da ita din, ta yadda wai gwamnati ba ta samun cikakkun kudin fiton da suka cancanta.
Irin wannan ojoro da coge a cikin harkokin tafiyar da tattalin arzikin kasar nan ba wani sabon labari ba ne, inda mutane suka kware wajen damfara, musamman gwamnatoci (a kan yi hakan da hadin bakin jami`ansu) a kan dukkan abin da za su gudanar muddin dai kudi za su gitta. Irin wannan ojoro da coge da sama da fadi a ke fama da shi akan bayar da kwangiloli da a ofishoshin da ake karbar duk wani nauyin kudin shigar gwamnati, kai hatta man fetur din kasar nan gurbatacce da tatacce haka ake fama da sama da fadin wanda ake hakowa ko wanda aka tace a cikin gida ko wanda aka yi odarsa, kamar yadda ta bayyana cikin rahoton Kwamitin tsohon dan Majalisar Wakilai Alhaji Faruk Lawan ya gano a kan biyan kudin sassaucin man fetur a shekarar 2012.  Kwamitin da rahotansa tsamiya ta juye da mujiya, daga karshe ta tabbata cewa shugaban Kwamitin ya karbi toshiyar baki ta Dala dubu 620, da aniyar ya fitar da sunan Kamfanin dan kasuwar man fetur din nan Macheal Otudola a kan samunsa da Kwamitin ya yi cikin jerin Kamfanonin man fetur da suka dade suna yi wa  gwamnatin ojoro da sama da fadi a kan makudan biliyoyin Naira a zaman kudin da take biyansu da sunan kudin sassaucin man fetur din da suke ta ikirarin sun shigo da shi.
Mai karatu, ka ga ke nan zargin da Hukumar ta Kwastam na hadin bakin da wasu jami`anta suke yi da wasu masu fasa kwauri, ba wani sabon labari ba ne a cikin cutar da ake yi wa gwamnatoci da sauran Hukumomi a kasar nan. Abin da `yan kasa suke tsammani ga wannan gwamnati, bisa ga irin yadda muke ganinta mai fada da cikawa, kamata ya yi ta tsaya tsaiwar daka wajen tabbatar da cewa jami`anta, musamman wadanda suke tsaron kan iyakokin kasar nan na kasa da ma ko ina, lallai su kara kula da yadda suke tafiyar da ayyukansu sosai da sosai tsakani da Allah.
Kafin lokacin da kuma kasar nan za ta iya wadata kanta da kanta da shinkafa, wadda gwamnatin ta yi aniyar hana shigo da ita kwata-kwata a shekarar 2018, lallai akwai bukatar gwamnatocin tarayya da na jihohi, har ma da na kananan hukumomi su tashi tsaye wajen tabbatar da cewa suna zuba makudan kudin don bunkasa ayyukan gona. Kasancewar masana tattalin arzikin kasa sun yi ittifakin cewa, tunda farashin man fetur ya fadi warwas, wanda dama daga kudinsa kasar nan take tinkaho, to ba wani zabi da ya rage illa a rungumi ayyukan gona.
Sai dai kuma kash! sai ga shi a kasafin kudin bana na gwamnatin tarayya da na jihohin kasar 30, (da aka iya samun alkalumman kasafin kudin su zuwa yanzu) mai jimlar Naira tiriliyan 12.2, duka-duka Naira biliyan 195.2 ko mu ce kashi 1.6 cikin 100, kacal suka ware don fannin ayyukan gonar da suka hada da sauran dawainiyar tafiyar da fannin ta yau da kullum. Adadin da ko kusa bai kai yawan 10 cikin 100 na yarjejeniyar da kasashen Afirka da ake yi wa lakabi da Yarjeniyar Moputu ta shekarar 2003, ta tanada kasashe su rinka kebewa a kasafin kudinsu, don inganta ayyukan gona. Kashin da ko kusa kasar nan ba ta taba warewa ba. Ka ga ke nan da wannan akwai jan aiki jajawur wajen ganin bunkasar ayyukan gona a kasar nan.