✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga

Ko dai ’yan bindigar su ajiye makamansu ko kuma mu ba za mu bar su ba.

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa sharaɗinsa na sulhu da ’yan bindiga shi ne kawai su daina kashe-kashe su zubar da makamai sannan su miƙa wuya.

A baya dai Gwamna Dare ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan fashin daji ba.

Ko a watan Yulin 2024, sai da wani mai magana da yawunsa, Alhaji Faruk Ahmad, ya bayyana cewa babu wani matsin lamba da zai sa gwamnatinsu ta yi sulhu da ’yan ta’addan.

Ya kuma jaddada cewa mataki ɗaya da gwamnatin ta ɗauka wanda kuma yana haifar da ɗa mai ido shi ne yaƙar ’yan bindigar amma babu batun sulhu.

Sai dai a hirarsa da BBC, Gwamnan ya bayyana cewa ba wai ba za a iya yin sulhu da ’yan bindigar ba ne, “amma ko da za ka yi sulhu ka yi shi a kan gaskiya, ai.

“Akwai da yawa waɗanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, bawai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba,” in ji Dauda.

Ya ƙara da cewa sai ’yan bindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.

Gwamna Dauda ya bayyana cewa suna samun nasara a yaƙin da suke da ƴanbindiga, “An kashe ’yan ta’adda fiye da 50 a ranar Juma’a a garin Tingar Fulani, wajen Zurmi da Shinkafi.

“Akwai manya-manyan kachalloli da yanzu haka sun tafi lahira, waɗanda suke tare da Bello Turji, akwai Sani Mainasara da Sani Black da Kachallah Auta, Audu Gajere da Kabiru Jangero, Dangajere da makamantansu, duk an hallaka su,” a cewar Dauda Lawal.

Gwamnan ya ce wannan nasara da ake samu za a ci gaba da samunta “har sai na kai ƙarshen lamarin. Ko dai su ajiye makamansu ko kuma mu ba za mu bar su ba.”

Matsin lamba ya sa ’yan bindiga neman sulhu — Makama

Fitaccen mai sharhi kuma masani akan sha’anin tsaro Zagazola Makama ya bayyana cewa matsin lamba da sojoji ke yi wa ’yan bindiga ya sa suke neman sulhu.

Zagazola ya bayyana haka a shafinsa yayin da yake sharhi akan wani faifan bidiyo da yake yawo, inda aka ji Bello Turji da wani shahararren malami a Zamfara, suna tattaunawa akan yadda ɗan bindigar zai ajiye makamai.

A baya-bayan nan, manyan ’yan bindiga da dama sun bayyana aniyarsu ta ajiye makamai sun rungumi zaman lafiya.