Gamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu zai saya wa kansa motocin alfarma na Naira biliyan daya da miliyan daya.
Kwamishinan Matasa, Jamilu Umar Gosta ne ya shaida wa manema labarai bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta jihar a karo na uku cewa majalisar ta aminta da sayawa ofishin gwamnan motocin alfarma na Naira biliyan daya miliyan daya da dubu 250.
A nasa jawabin, Kwamishinan yada labarai, Sambo Bello ya sanar cewa kudin da gwamnati ta ware wanda aka kawata titin gidan gwamnati ya lakume kudi miliyan 488.
Hanyoyi 39 da aka kawata da hasken wuta mai aiki da rana waton kuma ya lakume biliyan 1 da miliyan 756.
- Kotu ta tilasta gwamnatin Kano biyan diyyar rusau
- NNPP, PDP da wasu jam’iyyu 5 sun kulla ƙawancen siyasa
Ya ce akwai wasu hanyoyin mota biyar da aka kara za a a sanyawa fitillun, wanda aikin zai lakume miliyan 97.
Kwamishinan muhalli da gidaje Barista Nasiru Dantsoho ya ce gwamnatin za ta gina hanyoyi a unguwar Runjin Sambo kan kudi Naira Biliyan biyu.
Za kuma ta ta gina hanya kan titin Bodinga (gaban gonar Alu) kan kudi sama da Naira miliyan 816.
Haka ma majalisar zartarwa ta aminta da gina hanyoyi a unguwar Tudun Wada Unguwar Rogo a kan kudi biliyan 8 da miliyan 999, za a kammala aiki a cikin shekara daya.
An Kuma bayar da hanyar Gande zuwa Silame kan kudi sama da Biliyan 2.
Majalisar ta ware sama da biliyan 18 domin wadannan aiyukkan.