Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu ya sanar da soke duk wani mukami da tsohon Gwamnan Jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya yi tun daga 19 ga watan Maris, 2023, kuma ya fara aiki ne nan take.
Gwamnan ya kuma sanar da sauke sarakunan da tsohon Gwamnan ya nada a lokacin mulkinsa.
- Da wane aiki Kanawa za su rika tunawa da Ganduje?
- Kotu ta ba da umarnin mayar wa Muhuyi Rimin Gado kujerarsa
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Alhaji Abubakar Bawa, ya raba wa manema labarai a Sakkwato, ranar Talata.
A makon da ya gabata ne dai tsohon Gwamnan ya nada sarakunan, yana dab da sauka daga mulki.
Sanarwar ta ce an dakatar da sarakunan kuma za a waiwayi dakatarwa daga baya domin ci gaban jama’a.
Bawa ya kuma ce duk filayen da Tambuwal ya bayar a makwannin da suka gabata da duk kadarorin da aka yi gwanjonsu, an an soke su.
Kazalika, gwamnan ya soke dukkan ma duk sauyin sunayen makarantu da tsohuwar gwamnati ta yi, bai zauna ba, dukkan makarantun su koma a tsohon sunansu na baya.
Ya kuma ce ya sauke dukkan Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da ke rikon kwarya ya kuma umarce su da su mika ragamar mulkin ga Daraktocin Mulki. na Kananan Hukumomin.