✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da umarnin mayar wa Muhuyi Rimin Gado kujerarsa

Wata Kotu a Kano ta bai wa gwamnatin da Majalisar Dokokin Jihar umarnin mayar wa Muhuyi Magaji Rimin Gado kujerarsa ta shugaban Hukumar Yaki da…

Wata Kotu a Kano ta bai wa gwamnatin da Majalisar Dokokin Jihar umarnin mayar wa Muhuyi Magaji Rimin Gado kujerarsa ta shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar (PCACC).

Alkalin kotun, Ebeye David Eseimo ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.

A kwanakin baya ne dai kotun ta bai wa gwamnatin umarnin biyan Muhuyi hakkokinsa lokacin da ta sauke shi ba bisa ka’ida ba daga matsayinsa, tare da bayar da umarnin mayar masa da kujerar.

Sai dai duk da cewa gwamnatin karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta biya shi hakkokin nasa lakadan, amma ta yi mirsisi ta ki mayar da shi kan kujerar.

Bayan biyansa hakkokin nasa, Rimin Gado ya ce ya fara amfani da su wajen biyan kudaden magani a asibitoci da kayayyakin abinci ga talakawa.

Haka kuma kotun ta amince da bukatar Muhuyin cewa Majalisar Dokokin Jihar ba ta da hurumin korar mai kara ba tare da ta ji bayaninsa ba.

Haka kuma ta amince da batun korarsa da aka yi an yi shi ne ba bisa ka’ida ba, tare da bayar da umarnin a mayar da shi kan matsayinsa ba tare da bata lokaci ba.