✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Sakkwato ya kara wa ciyamomi wa’adin mulki

Rashin bayyana tsawon wa'adin da aka kara wa ciyamo a Jihar Sakkwato ya haifar da surutai

Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kara wa’adin mulki ga shugabannin ƙananan hukumomin jaihar su 23.

Gwamnan ya kara musu wa’adin ne kamar yadda dokar kananan hukumomi da aka yi ea gyaran fuska ta 2008 ta ba da dama.

Karin wa’adin zai bai wa hukumar zaben jiha damar shirya zaben shugabanni kananan hukumomi 23 da na kansilolinsu 244.

Sakataren yada labaran gwamnan, Abubakar Bawa, a bayanin da ya fitar, ya ce gwamnan ya taya murna ga shugabannin rikon kan karin wa’adin.

Ya ba su tabbacin ci gaba da goya musu baya su saukar da nauyin da aka dora musu.

Sakataren yada labarai na gwamnan bai ɗaga wayar wakilinmu ba domin sanin lokacin da aka kara musu ganin an ɓoye lokacin, abin da wasu ke ganin da akwai lauje cikin nadi.