✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Neja ya nada mata 131 a matsayin Hadimai

Gwamnan ya ce ya nada su ne saboda cika alkawarin yakin neman zabe

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya amince da nada mata 131 a matsayin Hadimai daban-daban a gwamnatinsa.

Kakakin Gwamnan, Balogi Ibrahim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar.

Balogi ya ce 41 daga cikin adadin, mata 41 sun rabauta da kujerun Ko’odinetoci ne, yayin da ragowar 90 din kuma Gwamnan ya nada su a matsayin manyan masu taimaka masa.

Gwamnan ya taya sabbin wadanda aka naɗa din murna sannan ya bukace Sudan su yi aiki tukuru wajen tabbatar da gwamnatinsa ta samu nasara.

Gwamna Bago ya ce ya yi nade-naden ne domin cika alkawuran da ya yi lokacin yankin neman zabe na ba mata damar bayar da gudunmawarsu ga ci gaban Jihar.