✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai nan da shekara 3 za mu sauka daga mulki – Gwamnatin sojin Nijar

Sojojin sun kuma ce duk wanda ya kai musu hari sai ya gane shafi ruwa ne

Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani, ya ce za su ci gaba da tafiyar da gwamnatin rikon kwarya har sai nan da shekara uku kafin su mika mulki ga farar hula.

Ya kuma gargadin cewa duk wanda ya kuskura ya kaddamar da kai wa kasarsa hari sai ya yi da-na-sani.

A cikin wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin din kasar a ranar Asabar, Tchiani ya ce,

“Babban burinmu shi ne mu kwace mulki, kuma duk wanda ya sake ya kai mana hari zai gane shayi ruwa ne.”

Gargadin nasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan dakarun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), sun ce a shirye suke su kutsa kai Nijar domin su dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a Nijar.

A cikin jawabin mai tsawon minti 12, Tchiani ya kuma ce, “Muna sanar da kafa wani kwamitin tattaunawa na kasa da zai fito da nagartattun hanyoyin samar da sabon Kundin Tsarin Mulki.”

Kazalika, ya yi jawabin ne jim kadan bayan tawagar ECOWAS karkashin tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta gudanar da tattaunawa domin warware rikicin siyasar kasar a birnin Yamai.

Tawagar ta kuma sami ganawa da hambararren Shugaban na Nijar, Mohammed Bazoum.