Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje marasa lafiya da kyautar Naira 20,000 kowannensu a babban asibitin Sunusi da ke garin Kano.
Gwamnan ya bai wa ɗaukacin marasa lafiyan da aka kwantar kyautar ce a lokacin ziyarar ba-zata da ya kai domin ganin halin da babbar cibiyar lafiyar take ciki.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Batun Satar Mazakuta
- Abin da ya sa a yanzu Buhari yake rayuwar nadama — Solomon Dalung
Sakataren Yada Labaran Gwamnatin Jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta bayyana bacin ran Gwamna Abba kan halin tagayyara da ya ga asibitin, inda ya ba da umarnin a yi masa kwaskwarima.
“Za a yi wa ɗaukacin asibitin gyara a dakunan matsa lafiya da banɗakuna da bangaren malaman jinya da ɗakunan tiyatar da sauransu, domin gaskiya abin da na gani ya tada min hankali,” in ji gwamnan, kamar yadda Sunusi ya nakalto.
Gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aikin gyaran domin samar da kayan aiki da kyakkyawan yanayi domin kula da lafiyar al’umma cikin sauki.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin ɗauka wata ma’aikciyar wucin gadi da ya samu tana kula da marasa lafiya a lokacin ziyarar tasa.