Rahotanni da ke fitowa daga Enugu sun ce a shekaranjiya Laraba Gwamnan Jihar Enugu Dokta Ifeanyi Uguanyi ya tallafa wa tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu da Naira miliyan 2 da dubu 700 a matsayin kudin magani.
Christian Chukwu da yanzu haka yake kwance a wani asibiti mai zaman kansa a Enugu, ya kamu da wata cuta ce da har yanzu ba a gano kanta ba.
Rahotanni sun ce tun farko shahararren dan kasuwar nan Femi Otedola ya yi alkwarin tallafa wa Chukwu da Dala dubu 50 kimanin Naira miliyan 18 don a fita da shi waje a nema masa magani, amma hakan bai yiwu ba. Ganin yadda ciwon ya fara cin karfinsa yana kwance a gida ba tare da ya samu wani dauki daga wajen kowa ba, ya sa iyalansa suka fara kokawa.
Wannan ne ya janyo hankalin Gwamnatin Jihar Enugu, ganin cewa Chukwu yana daga cikin jami’an da ke kula da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers mallakar jihar, sai Gwamna Ifeanyi Uguwanyi ya umarci a ba asibitin da aka kwantar da Chukwu Naira miliyan 1 da dubu 700 yayin da ya mika wata Naira miliyan 1 ga iyalansa don su ci gaba da rayuwa.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Enugu, Mista Ogbuagu Anikwe ya musanta rade-radin da ake yi cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da tsohon kocin Najeriya da Kenya, Christian Chukwu ba tare da an tallafa masa ba. Ya ce yanzu manuniya ta nuna, bayan Gwamnan ya bayar da wannan tallafi, kuma gwamnatin jihar a shirye take wajen daukar nauyin kocin zuwa kasar waje idan bukatar hakan ta taso don nema masa magani.
Christian Chukwu dai yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles kafin ya zama kocin kungiyar. Sannan ya taba horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Kenya da ake kira Harambee Stars.
Bayan shekaru sun yi nisa, yanzu haka tsohon kocin yana kwance ne a wani asibiti mai zaman kansa a Enugu yana karbar magani saboda rashin lafiyar da yake fama da shi.