An fara gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe a jahar Adamawa inda jama’a da dama suka halarci wajajen kada kuri’a fiye da yadda aka gudanar da kuri’un zaben a 18 ga watan Afrilu da ya gabata.
Kananan hukumomi 20 ne ake gudanar da zaben a wasu rumfuna 69, wadanda sakamakonsu zai tabbatar da wanda lashe zaben gwamna na 2023.
An fara kada kuri’u a rumfunan Ajiya 004 da 001 a Karamar Yola ta Arewa da rumfar Makama 002 da ke Limido Mustapha Aliyu na Yola ta Kudu da rumfar Kofar Bubajalo 001 a Karamar Hukumar Yola ta Judu.
Sai dai a Karamar Hukumar Numan da ake da rumfunar zazabe 14 kuma ake tsammanin samin kuri’u same da dubu bakwai.
A halin yanzu ba a ma kawo kayan gudanar da zane ba ballantana a fara maganar kada kuri’a.
A yau dai kananan hukumomi 20 ne za a gudanar da zabe; Demsa 1 da Ganye 1 da Girei 3 da kuma Gombi 1.
Sauran su ne Guyuk 2 da Hong 5 da Jada 1 sai Lamurde 3 da Madagali 1 sai Maiha 1.
Ragowar su ne Mayo Belwa 3 da Michika 7 da Mubi ta Arewa 6 da Mubi da Kudu South 2 da Numan 14 da Shelleng 3 da Song 4 da Toungo 2 da Yola ta Arewa 3 dai Yola ta Kudu 6.
Matakan tsaro kuma sun rufe duk wata mashigar da ke Yola domin ganin an gudanar da zabe a cikin wanciyar hankali da lumana.