An rantsar da Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Bala Ngilari a matsayin sabon Gwamnan Jihar Adamawa.
Mukaddashin Babban Jojin jihar, Mai Shari’a Ambrose Mammadi ne ya rantsar da sabon gwamnan, jim kadan bayan wata Babbar Kotu a Abuja ta zartar da hukuncin sauke Mukaddashin Gwamnan jihar, Umar Fintiri.
Tun da farko dai Mista Bala Ngilari ne ya shigar da kara a Babbar Kotun Abuja, inda ya nemi kotun da ta tabbatar masa da kujerar gwamna; inda ya ba da hujjar cewa takardar da ya gabatar da nufin yin murabus daga mukaminsa na Mataimakin Gwamna, gab da lokacin da za a tsige Gwamna Nyako ba ta bisa ka’ida.
Bukatar da Mista Ngilari ya gabatar wa kotu, ta dogare ne da ka’idar da tsarin mulki ya tanadar, cewa Mataimakin Gwamna zai iya yin murabus ne kawai bayan ya mika wa gwamnansa takardar neman haka.
A cikin karar ce Mista Ngilari ya nemi kotu da ta dakatar da hukumar zabe daga gudanar da duk wani zabe mai nasaba da kujerar gwamna a jihar, sannan kuma a bayyana shi a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa, a sakamakon tsige Murtala Nyako da aka yi a ranar 15 ga watan Yuli na bana.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Premium Times ta ruwaito, tun da farko, kotun ta ki amincewa da bukatar Mista Ngilari na cewa ta hana Hukumar Zabe Ta kasa daga gudanar da zaben cike gurbin kujerar gwamnan Adamawa. Shi kuwa, kasancewar ’yan majalisa sun tabbatar da murabus dinsa a ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata, sai ya kalubalanci murabus din nasa a kotun.
A karar tasa, wadanda yake kalubalanta sun hada da Umaru Fintiri, Shugaban Majalisar Jihar Adamawa da Majalisar Jihar ita kanta da Gwamnatin Jihar Adamawa da tsohon Gwamna Murtala Nyako da kuma Hukumar Zabe (INEC).
Mista Ngilari ya musanta cewa ya yi murabus daga mukaminsa gabanin karewar wa’adinsa, ya gindaya Sashi na 306 (1), (2) da (5) na kundin tsarin mulki a matsayin hujja. Ya ce wannan takarda da ya aika wa Shugaban Majalisa, ba yana nufin Majalisar jihar ta yi aiki da ita ba ne.
Kamar yadda ya ce: “Ni ban aika wata takardar yin murabus ga gwamna ko wani mutum na daban ba, in baya ga Shugaban Majalisar Jiha. Na aika takardar ne kawai ga Shugaban Majalisa amma ban aika ta da nufin ya yi amfani da ita ba bisa Sashi na 306 (1), (2) da (5) na kundin tsarin mulkin 1999 ba, domin kuwa ban aika takardar ga gwamna ba.”
A ci gaba da bayyana hujjojinsa a gaban kotu, Mista Ngilari ya zayyana dalilai bakwai, sannan ya nemi kotun da ta hana Hukumar Zabe Ta kasa ko wakilanta daga gudanar da zaben cike gurbin kujerar gwamnan da aka tsige. Haka kuma ya nemi kotun ta cire Mukaddashin Gwamna, Umaru Fintiri daga mukaminsa ba da bata lokaci ba. Daga nan ya nemi kotun da ta umurci Babban Jojin Jihar Adamawa ko Mukaddashinsa ko kuma Shugaban Kotun Gargajiya ko ta daukaka kara da ya rantsar da shi a matsayin gwamna.
Mai Shari’a Adeniyi Ademola ya amince da hujjojin Mista Ngilari, don haka ya zartar da cewa a rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa, sannan kuma ya umurci Hukumar Zabe Ta kasa Mai Zaman Kanta (INEC) da ta dakatar da gudanar da zaben cika gurbi da ta shirya gudanarwa a gobe Asabar.
Nyako ya yaba
Gwamnan Adamawa da aka cire Murtala Nyako ya yaba da hukuncin, ya ce hakan wata manuniya ce da ke tabbatar da cewa hanyoyi da aka domin tsige shi haramtattu ne da ke cike da hauragiyar siyasa.
Bayanin hakan yana kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da manema labarai na Nyako Ahmad Sanjoh ya raba wa manema labarai.
Murtala Nyako, wanda tun lokacin da aka cire shi yake zaune a kasar waje, tun farko bai yarda hanyar da mataimakinsa Ngilari ya bi ya yi murabus ba, domin kuwa ya ce kamata ya yi mataimakin nasa ya mika masa taklardar ajiye aikinsa , ba shugaban majalisa ba.
Y a yi nuni da cewa, hukunci wani mataki ne na farko da aka dauka na gyara kurakuren da majalisa ta yi, kuma ya yi imanin cewa kotu za ta tabbatar an yi rashin adalci wajen cire shi, wanda ya ce daidai yake da juyin mulki.‘’ Yanzu an fara daukar matakan gyaran haramtattun hanyoyin da aka bi wajen tsige gwamna kuma hakan zai ci gaba har sai gaskiya ta yi halinta Nyako ya koma gidan gwamnati a Yola.’’ Inji sanarwar.
Tsohon gwamnan sai ya taya Ngilari murna, tare da shawartarsa ya cigaba da nuna hakuri da tawali’’u yayin gudanar da aikinsa.
Hukumar zabe ta dakatar da zaben gwamnan Adamawa
Hukumar Zabe Ta kasa Mai Zaman Kanta, ta dakatar da gudanar da zaben cike gurbi na gwamnan Jihar Adamawa da ta yi shirin gudanarwa gobe Asabar.
Dakatar da zaben ya biyo bayan hukumcin Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, wacce ta zartar da dakatar da shi, tare da cire Mukaddashin Gwamnan jihar, Umar Fintiri.
A wata takardar da hukumar ta raba wa manema labarai, ta bayyana cewa ta dakatar da gudanar da zaben ne a sakamakon umurnin da Babbar Kotun ta Abuja ta ba ta. “A sakamakon wannan umurni na kotu, Hukumar Zabe (INEC) ta dakatar da duk wasu shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbin Gwamnan Jihar Adamawa, wanda aka sanya gudanarwa ranar Asabar 11 ga watan Oktoba, 2014.” Kamar yadda takardar ta sanar.
Umar Fintiri zai kalubalanci cire shi a kotu
Mukaddashin Gwamnan Jihar Adamawa, Umar Fintiri ya ce zai daukaka karar cire shi daga mukaminsa da kotu ta yi a Larabar da ta gabata.
Ya bayyana cewa tuni ya umurci lauyansa da ya daukaka kara ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Jam’iyyar APC ta yi maraba da tsige Fintiri
Jam’iyyar APC reshen Jihar Adamawa ta yi na’am da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a Larabar da ta gabata, na tsige Mukaddashin Gwamnan Jihar Adamawa, Umar Fintiri. Ta kara da cewa hukumcin wani abin ci gaba ne da ya kamata a yi maraba da shi a jihar.
Shugabar jam’iyyar ta jihar, Binta Garba ta bayana cewa a sakamakon wannan hukunci da kotun ta yanke, jam’iyyarsu na da karfin gwiwar cewa tsohon Gwamna Murtala Nyako, wanda shi ma yake kalubalantar tsige shi da aka yi a kotu, zai dawo kan mukaminsa.
A nasa bangaren, a yayin da yake murna da dakatar da zaben, Sakataren jam’iyyar PDP na Jihar Adamawa, Tahir Shehu ya ce, ko da an gudanar da zaben ko ma ba a gudanar ba, su dai jam’iyyarsu ta yi nasara.
Cigaba a shafi na 3