✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ya jinjina wa Hausawan Ile-Ife a kan hakurinsu

Gwamna Rauf Aregbesola na Jihar Osun ya jinjina wa al’ummar Hausawan garin Ile-Ife a kan rawar da suka taka lokacin rikici tsakaninsu da Yarabawa da…

Gwamna Rauf Aregbesola na Jihar Osun ya jinjina wa al’ummar Hausawan garin Ile-Ife a kan rawar da suka taka lokacin rikici tsakaninsu da Yarabawa da hakurin da suka nuna bayan rikicin, inda har suka shirya addu’o’in hadin gwiwa na Musulmi da Kirista domin samun zama lafiya a tsakaninsu.

Gwamnan ya ce yana sane cewa Hausawa mazauna Ile-Ife mutane ne masu son zama lafiya da ci gaba da rikon jama’a a matsayin ’yan uwa ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba. Saboda haka ya nemi su ci gaba da hakuri, musamman a kan rashin jin sakamakon binciken rikicin na bara.

 Bayanin haka yana kunshe ne cikin sakon da Mai ba Gwamnan Shawara a kan Harkokin kabilu a jihar, Alhaji Muhammed Bashir ya karanta a madadinsa a wajen taron addu’ar bude wasu ofisoshi da shaguna da aka yi musu kwaskwarima bayan lalata su a lokacin rikicin a Unguwar Sabo Ile-Ife.

“Gwamna Rauf Aregbesola ya aiko ni domin sanar da ku cewa bai manta da ku ba, yana jiran sakamako ne daga kwamitin da ya kafa domin binciken musabbabin rikicin da zai gano ainihin masu hannu wajen tayar da hargitsin da yawan mutanen da suka rasa rayuka da wadanda suka yi hasarar dukiya da za su samu tallafin gwamnati,” inji Mai ba Gwamna Shawara.

Majidadin Ile-Ife, Alhaji Malami Nasidi wanda ya mallaki shagunan da aka yi addu’ar budewa ya shaida wa Aminiya cewa, “Na yi hasarar dukiya mai yawa a lokacin rikicin da ya shafi mutanenmu. Na yi amfani da kudin aljihuna ne wajen sake gina shagunan da aka lalata mini. A matsayina na daya daga cikin ’yan Majalisar Sarkin Hausawan Ile-Ife, ina tabbatar maka cewa gaskiya ne mun samu tallafin Naira miliyan 21 da wasu bayin Allah suka bayar daga sassa daban-daban na kasar nan. Mun raba wannan kudi ga marayu da iyayensu suka rasa rayuka a lokacin rikicin da mutanen da suka yi hasarar kadarori, bayan lura da irin hasarar da kowa ya yi.”

“Akwai mutane masu yawa da suke rakuve da makwabta saboda kasa gina gidajensu da aka lalata. Saboda haka muke yin kira ga jama’a su kawo mana dauki, musamman wajen daukar nauyin aikin sake gyaran irin wadannan gidaje,” inji shi.

Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali da Mai ba Gwamna Shawara a kan Harkokin Malamai Cif Dauda Adefioye, ne suka jagoranci wadansu dattijan Hausawa da malamai zuwa wajen addu’ar.