Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa a ranar Asabar 26 ga Disamba 2020, zai sanya hannu kan kasafin 2021 na Naira biliyan dari da arba’in da miliyan talatin da hudu da dubu dari da tara da hudu da Naira arba’in.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar.
- Boko Haram ta kaddamar da hari a kauyen Adamawa
- 2023: Manyan ‘yan siyasa 4 sun sha alwashin kawo karshen siyasar Fintiri
Kasafin kudin da aka yi wa taken ‘Kwanciyar Hankali’, ya samu sahalewar Majalisar Dokokin jihar a ranar 24 ga Disambar 2020.
Gwamna Fintiri ya shirya yin bikin sanya hannu kan kasafin kudin a ranar Asabar a gidan gwamnatin jihar.
Ana sa ran cewar, kasafin kudin zai farfado da tattalin arzikin jihar, duba da yadda annobar COVID19 ta kawo koma baya a duniya.
Sannan ana fatar samun tagomashi kan abin da ya shafi harkar tsaro.