Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sake nada tsohon dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP, Ibrahim Kashim a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar, kuma nadin ya fara aiki ne nan take.
Bayanin nadin na kunshe ne cikin sanarwar da Mashawarcin Gwamnan Kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Alhamis.
- Rayuwar guragun Abuja a baca bayan shekara 15 da alkawarin gina musu mazauni
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Matasan Najeriya Ke Raina Jari
A cewar Gidado, an sake nada Kashim a mukamin ne duba da kwazonsa da sanin makamar aiki da kuma riko da gaskiya a bakin aiki
Batun nadin ya taso ne ’yan kwanaki bayan da Kashim ya janye kudirin takararsa bisa ganin damansa
Tun farko Kashim ya yi murabus daga mukaminsa don shiga takarar gwamnan jihar a PDP inda ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da kuri’a 655, yayin da Gwamna Bala Mohammed ya yi harin kujerar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar
Ganin ya fadi a zaben fidda gwanin takarar Shugaban Kasa a PDP, Bala Mohammed ya koma neman kujerar Gwmanan Bauchi karo na biyu a zaben 2023.
Ranar 4 ga Yuni ake sa ran Jam’iyyar PDP za ta sake gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamna a Jihar Bauchi inda take da Gwamna Bala a matsayin dan takara tilo.