✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Bala ne mafi dacewar Najeriya a 2023 —Matasan Arewa

Ta ce gwamnan na Bauchi ne mafi dacewa ya dare shugabancin Najeriya.

Wasu matasan arewa sun bayyana gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, a matsayin jagoran da ya fi dacewa da Najeriya a zaben 2023.

Mai magana da yawun kungiyar karkashin inuwar Kungiyar Masu Kishi ta CCLM, Kwamared Mujaheed Amin-Modibbo ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai ranar Asabar, a Kaduna.

  1. Dubun masu satar yara a akwatin gawa ta cika
  2. Ya Jagoranci Kai Farmaki Kayukan Zamfara Saboda Kama Mahaifinsa

A cewarsa, “Bala Mohammed ya nuna irin nagartarsa tunda ya fara siyasa daga matakin tarayya zuwa yadda ya sauya fasalin Bauchi bayan zamansa gwamna.

“Don haka muna rokonsa ya fito ya ceci Najeriya, saboda muradinsa na son hadin kai, bunkasa tattalin arziki a fadin kasar nan,” inji Modibbo.

Kungiyar wadda ta kunshi matasa daga bangarorin Najeriya daban-daban sun ce sun yi duba na tsanaki cikin jerin masu son yin takarar shugabancin Najeriya kuma babu wanda ya kai gwamnan dacewa.