✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hamisu: Marar hannaye da ke yin abubuwan da mai hannu bai iyawa

Ka san irin rayuwar da ake ciki yanzu masu lafiyar ma ba cikin sauki suke rayuwarsu ba, ballantana ire-irenmu.

Hamisu Musa, wani matashi ne ɗan asalin Jihar Bauchi da ya gamu da jarrabawar rasa hannuwansa biyu tun yana ɗan shekara 7 zuwa 8 a duniya.

Matashi wanda ya ce yana da burin zama lauya, yana yin wasu abubuwa na ban al’ajabi.

Aminiya ta ci karo da shi a garin Kafanchan a Jihar Kaduna a hanyarsa ta zuwa garin Lafiya, hedkwatar Jihar Nasarawa don rubuta jarrabawar NECO.

Ya ce ya biyo ta garin Zangon Kataf ne don duba ’yan uwansa a hanyarsa ta zuwa Lafiya.

Ya bayyana wa Aminiya cewa babu abin da ba ya yi na yau da kullum da ya shafi wanka da wanki da cin abinci da rubuce­rubuce a cikin waya da kira da amsa kira a waya da sauran abubuwa masu yawa.

“Har tsare-tsaren waya idan ta rikice wa mutum idan aka kawo nakan duba kuma in gano matsalar tare da gyarawa,” in ji shi

Hamisu ya nuna wa wakilinmu bidiyoyinsa da aka ɗauka yana gudanar da abubuwa daban-daban don kore shakku.

Daga cikin bidiyoyin akwai inda yake jan ruwa da inda yake wanka da wanki da kuma yadda yake cin abinci da sa tufafi, har ma da wanda yake kai ruwa ban-ɗaki da kansa.

Sannan ya gwada wa wakilinmu yadda yake rubutu da kafa tamkar mai yi da hannu.

“Burina a rayuwa shi ne in zama lauya. Na yi difloma a (Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci da ke) Misau (a Jihar Bauchi) ina son in yi digiri kan aikin lauya.

“Shi ne aka bukaci in gyara takardun jarrabawata na sakandare saboda in samu darasin Adabin Ingilishi (Literature) da zai ba ni damar wucewa kai-tsaye don karatun lauya,” in ji shi.

Ya ce ya fara sha’awar yin aikin lauya ne bayan kalllon wani fim ɗin Hausa da ba zai iya tunawa da sunansa ba, inda ya ga wani zalunci da aka aikata a ciki wanda daga nan ya fara tunanin yadda zai taimaka wa waɗanda ake zalunta a rayuwa.

Hamisu ya roki gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jama’a su taimaka masa wajen ganin ya cimma burinsa ta hanyar ɗaukar nauyin karatunsa da ɗawainiyarsa har ya kai ga gaci.

Ya ce, “Ka san irin rayuwar da ake ciki yanzu masu lafiyar ma ba cikin sauki suke rayuwarsu ba, ballantana ire-irenmu. Gaskiya zan so a tallafa min sosai.”

A ƙarshe ya yi kira ga matasa su tashi su nemi abin yi don rufa wa kansu asiri tare da amfanar al’ummar da suke rayuwa a ciki.