Gwamnatin Amurka da takwararta ta Koriya ta Kudu sun harba wani makami mai linzami a cikin teku a safiyar wannan Larabar.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga Koriya ta Arewa da ta harba na ta makami mai linzamin da ya ratsa sararin samaniyar kasar Japan.
- Buhari ya karrama dan sandan da ya ki karbar cin hancin dala dubu 200 a Kano
- ASUU na da hannu a rashawar da ake samu a bangaren ilimi —Buhari
Atisayen hadin gwiwar tsakanin sojojin Koriya ta Kudu da na Amurka, na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke shirin wani zama na musamman don tattaunawa kan abin da Koriya ta Arewan ta aikata ga Japan.
Majiyoyi daga bangaren Amurka da Koriya ta Kudu sun tabbatar da gwajin a ranar Laraba wanda suka harba makamin cikin tekun Yellow Sea kuma ya ci tazara mai tarin yawa.
Sai dai wata majiya daban ta bayyana yadda wani gwajin makami da sojin Koriya ta Kudun suka gudanar duk dai a yau din ya yi rashin nasara bayan da ya dawo jim kadan bayan harba shi sararin samaniya ko da ya ke babu wanda ya samu rauni.
Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuno yadda hayaki ke tashi da tartsatsin wuta a wajen da sojojin na Amurka da na Koriya ta Kudun suka gudanar da gwajin.
Har zuwa yanzu dai Koriya ta Arewan ba ta ce uffan game da gwajin nata na jiya da ta harba makamin mai cin matsakaicin zango ta sararin samaniyar Japan ba.
Gwajin na Koriya ta Arewa a jiya Talata, shi ne karon farko cikin shekaru biyar da ta harba makamin da ya ratsa sararin samaniyar Japan.
Wannan lamari dai ya sa gwamnatin Japan din bai wa mutane umarnin neman mafaka, baya ga kunna nata makaman masu linzami saboda kariya daga yiwuwar fuskantar farmaki.
Makamin mai linzamin wanda ya ci tafiya mai tazarar kilomita 4,500 zuwa 4,600 ya fada a Tekun Pacific.
Firaministan Japan Fumio Kishida ya yi tur da lamarin inda ya bayyana shi a matsayin ganganci.
Kwamitin Tsaron Kasa na Koriya ta Kudu ya bayyana matakin a matsayin babbar takala.