Wata guguwa tare da ruwan sama ta lalata gidaje da gine-gine sama da 200 a garin Misau, hedikwatar Karamar Hukumar Misau a Jihar Bauchi.
Aminiya ta gano cewa guguwar ta auku ne da yammacin ranar Lahadi.
- Dangote ya zo Legas shekara 45 da suka wuce ba shi da komai – Sanwo-Olu
- An yi wa tsohuwa mai shekara 80 fyade a Ondo
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Malam Kawu Mamuda, wanda dakunansa biyu suka rushe, ya bayyana cewa yana cikin tashin hankali game da inda iyalansaza su kwana kafin ya gyara gidansa.
“Uwargida tana tsaka da dafa abinci sai guguwar ta taso, sai da ta yi gaggawar kashe wutar da ta ke abinci da ita, sannan ta nemo yaran da ke wasa a waje, suna cikin dakin sai suka ji karar rushewar daya dakin. Da sauri suka ruga waje,” ya bayyana.
Wani da abin ya shafa, Bello Abubakar, ya ce ya kashe duk abin da ya tara domin gina gidansa da guguwar ta lalata.
“Na dauki hakan a matsayin wani abu da Allah Ya nufa, yanayin barnar da yawa, gidaje da dama sun lalace,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Mutane da yawa ba za su iya sake gina gidajensu ko gyara su ba, domin galibin wadanda abin ya shafa talakawa ne, ba su da karfin abincin yau da gobe ballantana gyara gida. Ya kamata hukumomin da abin ya shafa su kawo mana agaji.”
Da yake tsokaci kan lamarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bukaci wadanda abin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin kaddara, yayin da ya yi kira ga jama’a da su dasa itatuwa don rage aukuwar irin haka a gaba.
“Ina jajanta wa al’ummar Masarautar Misau bisa guguwar da ta lalata gidaje da dama da kuma asarar dukiyoyin jama’a.
“Domin hana gurbacewar muhalli, ina kira ga al’ummar Jihar Bauchi da su dauki dabi’ar dasa itatuwa da kuma adana wadanda suke da su,” in ji gwamnan.