✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dangote ya zo Legas shekara 45 da suka wuce ba shi da komai – Sanwo-Olu

Ya fadi haka ne yayin kaddamar da matatar man Dangote a Legas

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya je Jihar kimanin shekaru 45 da suka gabata ba shi da komai.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da yake jawabi yayin bikin bude matatar man fetur din da dan kasuwar ya gina a Jihar.

A cewar Gwamnan cikin raha, “Shekaru 45 da suka gabata, Dangote ya zo Legas ba shi da komai, amma yanzu shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka.”

Gwamnan ya kuma bayyana Dangote a matsayin dan kasuwar da sam ba shi da kabilanci kuma ya taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar.

Tun da farko da yake jawabi a wajen, Aliko Dangote, ya yaba wa Gwamnonin da suka shugabanci Jihar ta Legas tun daga kan zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu a 1999, har zuwa Sanwo-Olu na yanzu.

“Duka wadanda suka mayar da Jihar Legas garinsu kamar ni, za su tabbatar da cewa tun lokacin da aka dawo mulkin Dimokuradiyya, Gwamnatin Jihar ta yai tsayuwar daka wajen habaka kamfanoni masu zaman kansu.

“A kan haka nake mika cikakkiyar godiyata ga gwamnatin da ma Gwamnoninta saboda tsayin dakan da suka yi wajen bunkasa harkokin kasuwanci,” in ji Dangote.

Aminiya ta rawaito cewa bikin kaddamarwar ya sami halartar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da takwarorinsa na kasashen Ghana da Togo da Senegal da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar.