✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwa ta kashe yara 7 a Taraba

Guguwar dai ta biyo bayan wani ruwan sama da aka tafka a yankin

Yara bakwai ne suka rasu a garin Mutum-Biyu da ke Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba a sanadiyyar wata guguwar da ta biyo bayan ruwan sama.

Mummunar iskar dai ta biyo bayan ruwan saman da aka tafka a garin wanda kuma ya zama sanadiyyar rushewar gidaje masu yawan gaske.

Har wa yau, mutane masu yawan gaske sun samu raunuka sakamakon iftila’in.

Wani mazaunin garin na Mutum-Biyu mai suna Alhaji Yakubu Inuwa, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar kuma an yi asaran dukiya ta miliyoyin Naira ban sa asaran rayukan.

Iskar dai ta yi barna a garuruwan Mayoreneyo da garin Abba da Namne da Iware da Zangon Kwambi da suke yankin Kananan Hukumomin Gassol da Ardo-Kola.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ba a sami asaran rayukan a ragowar garuruwan ba.