Akalla mutum uku ne suka rasu a garin Takum da ke Jihar Taraba, sakamakon wata iska mai ƙarfi da ta riƙa kaɗawa a yankin har sau biyu cikin kwanaki biyu.
Wani mazaunin yankin, Malam Maiwada Takum, ya ce guguwar ta farko, ta auku ne da yammacin ranar Talata, inda ta rushe gidaje, makarantu da rumfunan kasuwanni da ofisoshi.
- Hotuna: EFCC Ta Gabatar Da Jami’in Kamfanin Binance A Kotu
- EFCC ta kama Bobrisky kan wulaƙanta takardun kuɗi
Maiwada, ya ce da farko an samu mamakon ruwan sama, sai kuma wata iska mai karfi wacce ta ɗauki sama da awa daya da rabi tana kaɗawa.
“Iskar ta yi muni, inda wasu gine-gine suka rushe sannan mutane da dama suka gigita, wasu suka maƙale a cikin ɓaraguzai. Iskar ta kashe wasu yayin da ta raunata wasu da dama.”
Yakubu Adamu wani mazaunin Takum, ya bayyana guguwar a matsayin wani iftila’i da ya shafe su.
James Gangum ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Taraba da kuma Hukumar Bada Agajin Gaggawa NEMA su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Mista Emmanuel Bello, babban mai taimaka wa Gwamna Agbu Kefas kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa na zamani, ya ce gwamnan ya je ziyarar jaje Takum domin duba irin barnar da guguwar ta yi.
A Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, nan ma an samu mummunar guguwa da ta yi ajalin mutum guda.
Lamarin ya faru ne ƙauyen Agbashi, da ke Karamar Hukumar Doma ta Nasarawa.
An ce aƙalla gidaje 100 suka lalace sanadiyyar guguwar da ta taso ta rusa babban masallacin ƙauyen da makarantar firamare ta garin.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Doma, John Bako-Ari ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai, inda ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talatar da ta gabata.
Anthony Oshinyeka, shugaban riƙo na kungiyar ci gaban Jama’ar Agbashi (ADA), ya bayyana alhininsa game da faruwar lamarin.
Ya kuma bayyana kaduwarsa game da mummunar illar da guguwar ta yi ga matsugunan Bassa da ke Iponu, inda mutum ɗaya ya mutu sannan wasu bakwai kuma suka jikkata.
Oshinyeka ya yi kira ga gwamnati da ta shiga lamarin cikin gaggawa domin taimaka wa mazauna yankin da abin ya shafa.
Ya kuma buƙaci gwamnati da masu hannu da shuni su gaggauta kawo agajin kayan jinya domin tallafa wa mutanen yankin da suka jikkata sakamakon ibtila’in.