Ranar Asabar din makon jiya ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bisa ga tanade-tanaden sashi na 99 (1), na Dokar Zabe ta 2010 (da aka yi wa gyara), wadda ta tanadi bayar da kwana 90 kafin zabe ga duk mai son ya tsaya takarar a cikin zaben kasa, ta sake busa usur ga dukan ’yan takarar mukamia gwamna da majalisun dokoki na jihohi su fara kamfe din neman kuri’a, don zaben badi. Zabubbukan da za a fara da na Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun badi, na gwamnoni da na ’yan majalisun dokoki na jihohi ya biyo baya da mako biyu.
Karatowar lokacin zaben ya sanya yanzu a kasar nan ba babban batun da yake daukar hankali sai yadda za a yi zabubbukan cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da tabbatar da adalci, wajen ganin duk wanda ya ci zaben an ba shi. Yin zabe cikin kwanciyar hankali da lunama da kuma tabbatar da cewa wanda duk jama’a suka zaba komai kashinsa da wadansu suke gani, to, lallai a ba shi nasararsa, hakan ne kashin bayan mulkin dimokuradiyya da ci gabanta da zaman lafiyar kasa da ta masu mulkin baki daya.
A irin wannan lokaci, manyan kasashen duniya irin su Turai da Amurka da kungiyoyinsu na ba da tallafi ta hannun USAID da DFID da sauransu. Bayan makudan kudade da kayayyakin aiki da sukan tallafa wa Hukumar INEC, sukan kuma shirya wa kungiyoyin kare dimokuradiyya da na ’yancin dan Adam da wakilan kafofin watsa labarai da su kansu jami’an Hukumar INEC da sauran masu ruwa-da-tsaki don tabbatar da mulkin dimokuradiyya da kuma ganin an yi zabubbukan lami lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana.
Bayan irin waccan gudunmawa daga irin wadancan kasashe da kungiyoyinsu, sukan kuma matsa gaba wajen yin gargadi da kakkausar murya da kira ga mahukuntan kasar nan, a kan lallai su tabbatar an gudanar da zabubbukan cikin kamanta gaskiya da adalci, wato a kiyayi magudin zaben.
Ko a kwanaki, bayan wani taro da suka yi a Abuja Kungiyar Tarayya Turai ta yi irin wancan kira, daga baya kuma Jakadan Birtaniya a kasar nan ya sake nanata bukatar a yin zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shi ma Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, bayan kiran hadin gwiwa da suka yi a wani taron kwamitinsu na tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristocin kasar nan a Abuja, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumar INEC, cewa lallai su tabbatar da gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a badi. Ko a ranar Juma’ar da ta gabata a wajen taron shekara-shekara na Kungiyar ’Yan uwa Mata Musulmi ta Kasa da aka gudanar a Abuja, a sakon da ya aike wajen taron ta hannun Mai martaba Sarkin Keffi Dokta Shehu Chindo Yamusa, sai da Mai alfarma Sarkin Musulmi ya sake nanata wancan kira na lallai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da an gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe da zai da dace da kudirin Majalisar Dinkin Duniya.
Ita ma Rundunar ’Yan sandan Najeriya da kwamishinonin ’yan sandan jihohi a ’yan kwanakin nan ba abin da suka sa a gaba da ya wuce yin tarurruka da shugabannin jam’iyyun siyasa da kungiyoyin kare mulkin dimokuradiiyya da sauaransu inda suke gargadin lallai su tabbatar an yi zabubbukan cikin kamanta gaskiya ba tare da magudi da ka iya kawo tashe-tashen hankula da zubar da jini ko asarar rayuka ba.
A irin waccan ganawa an ruwaito Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas, Mista Imohidi Edgal bayan wani taro da suka yi da Hukumar INEC, yana cewa rundunarsa ta gano wuraren da aka fi aikata ta’asa a jihar, yana mai ba da tabbacin cewa tun daga yanzu za su karfafa sintirin hadin gwiwa, musamman a cikin Kurmi da bakin teku, su da dukan jami’an tsaro da ke jihar don samun nasarar babban zaben na badi in Allah Ya kai mu.
A Hukumar Yi wa Kasa Hidima (NYSC), hukumar da akasarin jami’anta (’yan hidimar kasa) suke zama Turawan zabe na gindin akwati, a ’yan kwanakin nan ana ta jin amon Darakta Janar dinta Birgediya Janar Suleiman Kazaure, duk inda ya kai ziyara ko ya tura wakili a sansanin ’yan hidimar kasar, maganarsa ba ta wuce kada su kuskura su hada kai da ’yan siyasa su yi magudin zabe. Ya kan sanar da masu hidimar kasar cewa “Idan ’yan siyasasuna son kwace akwati ko kayayyakin zabe daga wajensu, kada su kuskura su ja da su, kuma taimaka musu wajen sa kayayyakin a motocinsu, don ku kauce wa duk wata matsala.
Dukan wadannan kiraye-kiraye da fadakarwa suna zuwa ne kasancewar an shiga kakar zabubbukan badi, kakar da ta faro tun daga lokacin da jam’iyyun siyasar suka gudanar da zabubbukan fitar da gwanayen da za su tsaya musu takara a watan Oktoban da ya gabata. Zabubbukan fitar da gwanin sun rika haddasa husuma da kashe-kashen jama’a hatta a cikin jam’iyya daya, kamar yadda ya faru a Jihar Zamfara inda aka kashe magoya bayan ’yan takarar neman mukamin Gwamnan jihar a Jam’iyyar APC da suke adawa da Gwamnan Jihar.
A tawa fahimtar, samun sahihi kuma ingantaccen zabe bai rataya a kan mutum daya ko wata hukuma daya ba, ya rataya ne a kan duk wani dan kasa nagari. Ina sane da cewa duk jam’iyyar da ke da gwamnati ita ake kira da lallai ta tabbatar da samun nasarar zabubbukan, bisa ga yadda ake ganin za ta iya sarrafa jami’an tsaro da na Hukumar INEC da kuma lalitar gwamnati da ke hannunta. Don haka ke nan ita ke da wukar yankan nama, alhali an manta cewa a jihohin da jam’iyyun adawa ke mulki haka za ka tarar gwamnoni na juya irin wadancan jami’ai, don su kai ga nasara. Wato ke nan shi magudin zabe a kasar nan dama ce, ma’ana kowane gauta ja ne.
A ganina daga fara wannan jamhuriyyar, ya isa kowa ya natsu a daina magudin zabe. Ba don komai ba sai don ganin idan don ka zama ubangida ke sa ka tsaya kai da fata sai ka murde zabe, zuwa yanzu kowa ya ga yadda ake kai ruwa-rana har ta kai ba a ga maciji a siyasar ubangida da yaron gida. Idan kuma banga kake yi don in an ci a yi maka wani abu, zuwa yanzu mun ga wadanda suna wata uwa duniya ake hayaniyar zaben, bayan an kafa gwamnatin haka siddan an kira su ana yi da su. Ashe ke nan kyautuwa ya yi kowa ya sa ransa a inuwa ya bari a yi zabe lami lafiya.