✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudun Mita 100: Najeriya ta gaza cin lambar zinare a karon farko cikin shekara 50

A karon farko cikin shekara 50 da fara Gasar Wasanni ta Afirka a shekarar 1965, Najeriya ta gaza cin lambar zinare a gasar gudu ta…

A karon farko cikin shekara 50 da fara Gasar Wasanni ta Afirka a shekarar 1965, Najeriya ta gaza cin lambar zinare a gasar gudu ta mita 100 ta mata da aka kammala a ranar Litinin da ta gabata a Kongo.
’Yar wasan gudu mace ta kasar Kwaddibuwa Marie-Josee Talou ta doke wakiliyar Najeriya Damola Osayomi.
Osayomi who won the wadda ta ci lambar zinare a Maputo ta bace daga filin da kuma kasar Kongo bayan da Josee Talou ta doke ta tare da kafa sabuwar bajinta ta kare gudun a cikin dakika 11.02 a ranar Litinin.
Magujiya ’yar Najeriya Mercy Nku ce ta rike bajinta ta dakika 11.03 na tsawon shekara 16 kafin ’yar Kwaddibuwar mai shekara 28 ta karya bajintar inda ta rubuta tarihinta a wasan gudu na Afirka.
’Yan wasan gudu mata na Najeriya da suka hada da Blessing Okagbare da Gloria Asunmu da suka lashe lambobin azurfa da tagulla a gasar ta Maputo sun janye daga gasar daf da za a fara ta, yayin da Cecilia Francis da ta shiga gasar ta zo na biyar da dakika 11.53.
’Yar wasan gudu ta kasar Kenya Eunice Kadogo da ta lashe lambar azurfa a gudun mita 100 na matan ita ma ta kafa sabuwar bajinta inda ta kare a dakika 11.47, yayin da Pon Karidjatou Traore ta kasar Burkina Faso ta lashe lambar tagulla da dakika 11.49.
Kwaddibuwa ce ta kuma lashe gasar gudun mita 100 ta maza bayan da Ben Youssef Meite ya doke Ogho Oghene Egwero na Najeriya a fafatawar da ta burge jama’a.  Youssef Meite ya kafa sabuwar bajinta ta kammala gudun a dakika 10.04 inda ya samu lambar zinare, yayin da Egwero ya kare a dakika 10.17 ya samu lambar azurfa, sannan wani dan Kwaddibuwa mai suna Koffy Wilfried Hua ya lashe lambar tagulla, yayin da wanda ke rike da kambain gudun mita na Najeriya, Seye Ogunlewe, ya kare gudun a matsayi na biyar.