Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara sun tuntube su.
Masari ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi ba Shugaba Muhammadu Buhari bayani game da halin da ake ciki kan daliban da aka dauke a makarantar.
- Yadda na kubuta daga hannun ’yan bindiga —Dalibin GSSS Kankara
- Sojoji sun zagaye dajin da aka kai daliban da aka sace
- Majalisar Dinkin Duniya na bukatar a gaggauta sako daliban makarantar Kankara
“Gwamnan wanda Mataimakinsa, Manir Yakubu, ya yi wa rakiya, ya ce masu garkuwa da daliban sun tuntube su kuma ana magana da su kan dawo da yaran cikin koshin lafiya”, inji sanarwar da kakakin Shugaba Kasa, Garba Shehu, ya fitar.
Garba Shehu ya ci gaba da cewa: “Gwamna Masari ya kuma tabbatar da wa Shugaba Buhari da cewa hukumomin tsaro sun gano inda aka kai daliban”.
Gwamnan ya ziyarci Buhari ne a Daura ranar Litinin domin bayani game da daliban da aka sace inda ya ce ana samun nasara a kokarin da ake yi na kubutar da su.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’a da dare ne ’yan bindiga suka far wa makarantar GSSS Kankara suka yi musayar wuta da ’yan sanda masu gadi.
A harin ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da dalibai da kawo yanzu ake ta samun bayanai masu karo da juna game da adadinsu.