Ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa, Antoine Griezmann, ya yi ritaya daga murza wa ƙasarsa leda.
Ɗan wasan mai shekaru 33 a duniya, ya bayyana haka ne a ranar Litinin.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun ceto mutum 40 a jihohi 4
- Matashi ɗan Jihar Yobe na gab da ƙwace kambin Gwarzon Ɗaukar Hoto na Duniya
Griezmann ya shafe shekaru 10 yana buga wa Faransa ƙwallo, inda ya buga wasanni 137.
“Zuciya cike da ɗimuwa nake sanar da rufe babin rayuwata da Faransa,” kamar yadda ya wallafa a shafin X (Twitter).
Ɗan wasan gaban na Atletico Madrid, ya fara buga wa Faransa wasa a watan Maris ɗin 2014, inda ya buga wasanni 14 tare da jefa ƙwallaye 44.
Griezmann shi ne ɗan wasa na huɗu daga cikin ’yan wasan da suka fi jefa wa Faransa ƙwallo a raga, inda yake bin bayan Olivier Giroud, Thierry Henry da kuma kyaftin ɗin tawagar Kylian Mbappe.