Waiwayen baya a rayuwar mutum abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwa. A wannan wake mai taken ‘Godiya Ga Kowa’ Bashir Yahuza Malumfashi ya waiwayi baya, inda a shekarun biyu da suka gabata, ranar Talata, 11-04-1348 (BH), daidai da 10-01-2017, ya samar da wadannan baitocin:
Da sunan Allah na fara,
Wanga aiki ni na tsara,
Fa’idarsa domin ta dora,
Ta zarce ko ko ta zarra,
Ga alheri ba da jinkiri ba.
Aminci ga baban Zahra,
Yabo ga mai hana zara,
Daha ka yo masu zarra,
Nufinka a daina sharra,
Yabonka ba a kwauro ba.
Godiyata ga Jalla mara,
Da Ya yo ni babu tara,
Ya hana a yo min kyara,
Ga tunani domin in gyara,
Shukura ba za ni bari ba.
Godiya ga iyalaina,
Ku ke jure jidalina,
Kuna ta goyon bayana,
Addu’arku tana bina,
Kula ku ban daina ba.
Gaisuwa ga ku dangina,
Ku tsatso ne na jinina,
Kun damu da tohona,
Kuna ta yin mararina,
Zumunci ba zan daina ba.
Gare ku zumun aikina,
Hadin kai kun yo guna,
Loton wahala ko murna,
Burinmu mu hano barna,
Godiyarku ba zan fasa ba.
Ku kuwa masoyana,
Na dukka kusurwoyina,
Na nesa da nan gibina,
Jinjinarku tana kallona,
Kaunarku ba zan fasa ba.
A haguna akwai damana,
A farina har ma da bakina,
Duniyarmu kala biyu ce juna,
A gare ku ku makiyana,
Kyararku ba ta karyan ba.
Ku sani Allah Ne gatana,
Shi Ke tafiyar duk lamarina,
Shi Ke karen fitinonina,
Ko kun taru kuna cizo na,
Kariyar Allah ba ta kare ba.
Komai zagi kan lamarina,
Komai ku kin harkokina,
Ba kwa iya ture lokacina,
Ko ko ku datse numfashina,
Ikon Allah ba zai kare ba.
Na gode wa Allahna,
Na yaba wa Manzona,
Nai addu’a ga iyayena,
Godiya gare ku zumaina,
Jinjina a gare ku ba na fasa ba.