✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a kaddamar da Matatar Man Dangote

Ita ce matatar mai mafi girma a nahiyar Afirka, inda za ta samar da tataccen mai ga kasashe 12

A ranar Litinin Shugaba Buhari zai kaddamar da matatar mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.

Ana sa ran matatar, kai karfin samar da samar da ganga 650,000 na tataccen mai a kullum za ta biya wa Najeriya bukatunta na man fetur da sauran dangoginsa 100 bisa 100.

Akwai kuma hasashen ‘yan kasar za su samu sauki daga abubuwan da matatar za ta rika samarwa irin su kananzir da man dizel da man jirgin sama da man fetur da dai sauransu.

Haka kuma ana hasashen za ta samar da Dala biliyan 21 — kimanin Naira tiriliyan 9.7 — a shekara, a bangaren danyen mai, duk da cewa sai nan gaba a cikin wannan shekara matatar za ta fara aiki.

Rahoton cibiyar S&P Global Commodity Insights mai nazari kan cinikayya ya nuna a cikin watan Yuni mai kamawa Matatar Mai ta Dangote za ta fara samar da tataccen mai.

‘Yan Najeriya na murnar ganin fara ikin matatar wadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) ke da kashi 20 cikin 100 na hannun jari.

Masu ruwa da tsaki a bangaren mai na ganin matatar za ta sauya matsayin Najeriya daga mai shigo tataccen mai, zuwa mai fitarwa kasashen waje.

Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke shirin soke tsarin biyan tallafin mai wanda kudin da take kashewa a kai y karu daga biliyan N351 a 2005 zuwa tiriliyan N4.39 a 2022, kafin ya karu zuwa tiriliyan N3.6 a watanni shida na farkon 2023.

Duk da cewa babu tabbacin fara aikin matatar zai rage tsadar mai a kasar, zai rage kudin da ake kashewa wajen jigilar man a irin asarar da ake yi.

Wasu masana na ganin za a saumu saukin farashin mai idan har gwamnatin Najeriya za ta ba wa matatar danyan mai a farashi mai sauki; sai dai kuma kamfanin mai bukaci haka ba tukuna.

Wasu masanan kuma na ganin fara aikin matatar zai bude wani sabon babi a kan batun tallafin da gwamnati ke neman cirewa.

Shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN), Kwamred Festus Osifo, ya ce fara aikin matatar zai rage kudaden da ake kashewa wajen shigo da tataccen mai da rashin tabbacin farashinsa.

Asusun Lamudi na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa fara aikin Matatar Mai ta Dangote zai daimaka wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

Kungiyar masu samar da man fetur ta Afirka (APPO) ta ce matatar za ta rika samar da mai ga kasashe 12 da kuma kashi 36 na man da ake bukata a nahiyar, wanda hakan zai rage kudin da ake kashewa wajen shigo da man.