✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane da dama sun kone a hatsarin tankar mai a hanyar Abuja

Ana fargabar mutane da dama sun kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi bayan wata babbar mota makare da man fetur ta yi hatsari

Ana fargabar mutane da dama sun kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi bayan wata babbar mota makare da mai ta yi hatsari a hanyar Lakwaja zuwa Abuja a safiyar Lahadi.

Shaidu sun shaida wa wakilinmu cewa hatsarin ya faru ne bayan tankar da ke dauke da man ta kwace wa direbanta, ta yi taho-mu-gama da wata mota da ta taho ta daya hannun.

A lokacin da wakilinmu ke tattaunawa da wani ganau mai suna Yusuf ya shaida mana cewa, “Tankar fetur din da sauran motocin da abin ya rutsa da su suna kan ci da wuta, ciki har da wasu bas din haya da karamar mota

“Jami’an tsaro da na hukumar kiyaye haddura suna ta kokarin kashe gobarar.”

Yusuf ya ce da misalin karfe 7 na safe aka yi hatsari.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen Jihar Kogi, Stephen Dawlung ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun isa wurin domin shawo kan lamarin

“Tankar fetur din tana kan ci da wuta, lamarin da ya kawo cinkoson ababen hawa. Zuwa yanzu dai ba mu da cikakken bayani, sai nan gaba”, in ji shi.