✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar rukunin Premier a Ingila da kuma La-Liga a Sifen

A gobe Asabar 17 ga wannan wata  ne ake sa ran za a fara kakar wasanni ta bana a kasashen Ingila da kuma Sifen.A Ingila,…

TUNA BAYA:  Kocin Manchester United Sa Alex Ferguson (a tsakiya) tare da Cristiano Ronaldo (a dama) a lokacin da ya sayo dan wasan daga kulob xin Sporting Lisbon da ke Fotugal Fam miliyan 12 a shekarar 2003.  A lokacin Ronaldo yana da shekara 18.A gobe Asabar 17 ga wannan wata  ne ake sa ran za a fara kakar wasanni ta bana a kasashen Ingila da kuma Sifen.
A Ingila, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce za ta kare kambunta bayan ta lashe kofin a bara.  Kuma za ta fara wasanta na farko ne da kulob din Swansea.
Sai dai a wannan karon ana ganin kulob din ba zai sha ta da dadi ba ganin yadda kungiyoyin kwallon kafa irin su Manchester City da Chelsea da Arsenal da Liberpool da sauransu suka zage damtse na ganin sun karbe kofin daga gareta yayin da kulob din United yake ganin har yanzu akwai sauransa a fagen kwallo.
A kasar Sifen kuwa, kulob din FC Barcelona ne zai kare kambunsa bayan lashe kofin a kakar wasan da ta wuce.
Babbar abokiyar hamayyarta a Sifen watau Real Madrid ta sha alwashin karbe kofin daga wajen Barca a kakar wasa ta bana musamman ganin yadda ta yi cefanen ’yan kwallon da take ganin za su taimaka mata wajen cimma burinta a wannan lokaci.
Mafi yawan masu sha’awar kallon kwallo a nan Najeriya sun fi sha’awar kallon gasar rukuni-rukuni ta Ingila da aka fi sani da Premier da kuma ta La-Liga da ke Sifen.
Akwai hasashen gidajen kallon kwallo za su rika cika fiye da bara musamman ganin yadda masu sha’awar kallon kwallo suke dokin ganin yadda kakar wasannin za su kaya.