’Yan kwana-kwana kusan 300 ne ke kokarin kashe wata gobarar daji da ta tashi tun ranar Litinin ta kuma ci gaba da ci har Talata wacce ta kone gidaje akalla 60 a Kudancin Rasha.
A cewar wasu rahotani na kafefen yada labarai na yankin, gobarar ta tashi ne tun a ranar Litinin daga dajin Ust-Donetsk da ke Arewacin Rostov, ta kwana tana ci a inda ta kone gidajen jama’a.
- Za a sami ambaliyar ruwa a Sakkwato, Kebbi da Borno kwanan nan – NiMet
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9, ya jikkata 13 a Bauchi
Gobarar ta kone kimanin hekta 136 na filayen noma a safiyar ranar Talata, a inda ta yi barna a wasu kauyuka uku.
Kamfanin dillacin labarai na gwamnatin Rasha TASS ya ce, Ma’aikatar bayar da Agajin Gaggawa ta kasar, ta sanar da cewa, ta kwashe ilahirin mazauna kauyukan zuwa tudun mun tsira.
Ma’aikatar ta samar da jirgi mai kashe gobara da karin wani jirgin mai saukar ungulu guda daya da masu aikin kashe gobara 300 da kuma kayayyakin aikin kashe gobara daban-daban har guda 90.