Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa.
Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka.
Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba.
Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.”
- Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa
- NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa
Ya ƙara da cewa suna ƙera jiragen ne ta hanyar inganta ayyuakansu daga abin da aka saba.
Ya ce, “yanzu muna aikin ƙera jirage marasa matuƙa da helikwafta ’yar Najeriya da sauransu.
“Wasu daga kayayyakin da muke amfani da su an ƙera su ne a ƙasashen da suka ci gaba.
“Ta hanyar aikin injiniya da ƙwarewar kimiyya muka hada waɗanna kayayyaki da na’urori,” in ji shi.