Rasha ta zargi Ukraine da kai mummunan hari da jirage sama marasa matuka kan shalkwatar jiragen ruwan yakinta da ke garin Sevastopol da ke bakin gabar teku.
A cewar jami’an Rasha, An soma kai harin ne da misalin karfe 4:20 agogon kasar a inda jiragen sama marasa matuka suka soma luguden wuta.
- Jirage marasa matukan Rasha sun yi wa Ukraine ruwan bama-bamai
- Rasha ta ba da umarnin kammala gyaran gadar Crimea a wata 7
Gwamnan yankin wanda Rasha ta nada, Mikhail Razvozhaev, ya ce, sojojin ruwan Rasha sun mayar da martanin harin, inda suka kakkabo jiragen saman marasa matuka.
A cewarsa, wannan hari shi ne mafi girma da aka kai wa Rasha a yankin tun lokacin da ta shiga yankin na Krimea a watan Fabrairu.
A harin an lalalata akalla jirgin ruwan yakin Rasha guda daya, sannan babu wani gini na farar hula da harin ya shafa.
Garin Sevastopol shi ne gari mafi girma a yankin Krimiya da Rasha ta kwace a hannun Ukraine a shekarar 2014.